1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fiye da mutane 180 sun mutu a rikici

Suleiman Babayo AH
April 18, 2023

Fiye da mutane 200 sun halaka sakamakon rikicin Sudan tsakanin sojoji da mayakan kungiyar tsaro ta ko ta-kwana (RSF) da ake kira mai mayar da martanin gaggawa yayin da wasu mutane kimanin 2,000 suka jikata.

Sudan I Birnin Khartoum na Sudan da yaki ya lalata
Khartoum babban Sudan da yaki ya lalataHoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Rahotanni daga kasar Sudan na nuni da cewa fiye da mutane 180 suka halaka yayin da wasu kusan 2000 suka jikata sakamakon artabu da ake ci gaba da fafatawa tun karshen mako tsakanin sojojin kasar da dakarun hukumar tsaro mai karfi.

Shugaban mayakan kungiyar tsaro ta ko ta-kwana RSF, mai karfi, Janar Mohamed Hamdan Dagalo wanda aka saninsa da Hemedti ya tabbatar da shirin dakarun na mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwana daya domin fararen hula da rikicin ya ritsa da su samu hanyar ficewa. Wasu rahotannin kafafen yada labarai na kasashen Larabawa sun nuna cewa yarjejeniyar ta fara aiki, inda lamura suka lafa bayan fafatawa tun ranar Asabar da ta gabata.

Sai dai Janar Hemedti ya zargi sojoji da rashin mutunta yarjejeniyar wajen kai hare-hare yankunan da ke shake da fararen hula.

Wannan rikici na Sudan ya samu asali sakamakon sabani tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan shugaban hafsoshin soja kuma shugaban gwamnatin rikon kwarya da shugaban mayakan kungiyar tsaro ta ko ta-kwana RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo  kana mataimakin shugaban gwamnatin.