1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Rikici tsakanin sojojin Kwango da 'yan tawaye

November 12, 2023

Akalla mutane shida sun mutu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sannan wadansu da dama sun jikkata a yayin wani rikici da ya barke a tsakanin sojojin gwamnati da mayakan sa kai da ke dafa masu a Gabashin kasar.

Jayaya tsakanin sojojin Kwango da mayakan sa kai
Jayaya tsakanin sojojin Kwango da mayakan sa kai Hoto: Zanem Nety Zaidi/DW

Lamarin ya auke ne da Yammacin jiya Asabar a wani kauye da ake kira Mugerna da ke a tazarar kilomita 15 daga Goma babban birnin lardin Kivu ta Arewa kamar yadda majiyoyi daga mahukuntan yankin suka tabbatar.

Karin bayani:  Kwango: Fada ya barke a Arewacin Kivu

Wata majiya daga rundunar tsaron Kwango da ta bukaci a sakaya suna ta shaidar da cewa rundunar sojan ta yi artabu ne da mayakan kungiyoyin sa kai da ake kira ''Wazalendo'' sai dai har yanzu ba a kai ga tattara alkaluma a game da yawan wadanda lamarin ya shafa ba.

Karin bayani:  Kawo karshen ayyukan rundunar MONISCO a Kwango

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwabza fada da 'yan tawayen M23 da ke tayar da kayar baya a Arewacin Goma tare yin ajalin mutane da dama baya ga tilasta wa wadansu dubbai tserewa daga matsugunnensu.