Rikici ya kara kamari a jam'iyyar PDP
May 30, 2013A yayin da fastocin yakin neman zaben shugaban Najeriya na gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da gwamman jihar Rivers Rotimi Amaechi su ka bayyana a Abuja, tsohon shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo, ya fito karara yace Lamidon fa zai iya, a yanayin da ke nuna kara raba gari tsakanin Obasanjon da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a game da zaben 2015. Ko wane tasiri wannan ke da shi ga siyasar Najeriyar kanta?
To ana dai kara jan daga da ma shan damara na irin fafatawar da zata faru a jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya a zaben 2015 da tuni aka kada kugensa a cikin kasar, domin kuwa kalaman da tsohon shugaban Najeriyar Cif Olusegun Obasanjo ya yi da yace lallai gwamnan jihar Jigawa zai iya, ya nuna inda ya karkata akan wannan batu.
Bayanar fastocin kamfe na yakin menan zaben zama shugaba kasa na gwamnan jihar Jigawan Sule Lamido da abokin takarasa Rotimi Amaechi lokaci kalilan bayan kalaman da shugaban Obasanjo ya yi kansa na nuna cewa zai iya ya sanya tambayar tasirin da wannan ka iya yi ga fagen siayar Najeriyar? Dr Usman Muhammad masanin kimiyyar siyasa ne da ke Abuja.
Sanin irin matsayi da ma tasirin da ake hangen Obasanjo na da shi a jam'iyyar ta PDP da ya kasance uban gida ga shugaba Jonathan kafin daukan wannan sabon matsayin, da kuma rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameachi da aka nuna shi a mastayin abokin takarar Alh Sule Lamidon, na nuna irin fafatawar da za ta iya faruwa siyasar Najeriya musamman ma dai a zaben 2015. To sai ga Dr Yunusa Tanko shugaban kungiyar jam'iyyun siyasun Najeriya, kuma ma shugaban jam'iyyar adawa ta NCP na mai cewa akwai bukatar yin taka tsan-tsan don kada kilu ta jawo bau.
Sauya matsayi da ma daukan wani sabon yaron gida da Obasanjo ke kara fitowa fili ya nuna babbar baraka a jam'iyyar PDP.Sakataren jam'iyyar PDP Cif Olagunsoye Oyinlola da tuni ya rumta zuwa kotu na nuna alamun kama hanyar ta ware ko ta waraya a tsakanin sassan biyu da ke girgiza jam'iyyar PDP da ma inda ta dosa.
Abin jira a gani shine tasirin da wannan ka iya yi ga siyasar Najeriyar da ta kwashe shekaru 14 tana hannun jam'iyya mai mulki, duk kuwa da kishirwa da jam'iyyun adawa ke nunawa na kaiwa ga madafan ikon kasar, da har yanzu ba'a taba gani balle samun dandana hakan ba.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Yahouza Sadissou Madobi