1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barayin shanu sun kashe mutane 38 a Najeriya

Abdul-raheem Hassan
December 19, 2021

Rahotanni daga arewacin Najeriya na cewa barayin shanu sun halaka mutane 38 a wasu hare-hare uku da suka kaddamar a jihar Kaduna.

Nigeria Kaduna | Polizeieinheit steht Wache in Unguwar Busa
Hoto: Christina Aldehuela/AFP/Getty Images

 

Kwamishinan harkokin cikinj gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce maharan da suka saba ta'addanci da babura sun farwa kauyukan Kauran Fawa da Marke da Riheya a gundumar Giwa, maharan sun kona gidaje da ababen hawa tare da lalata amfanin gona da dama.

Arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya na fama da gungun barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, matakin da ya tunzura kungiyoyi fara zanga-zangar kira ga hukumomi a kawo karshen matsalar zubar da jini a kasar.