Rikici ya sake ɓarkewa a Yemen
August 21, 2011Majiyoyin ƙabilu daga ƙasar Yemen sun bayyana cewar mutane 11 ne suka mutu sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake guda biyun da ake zargin ƙungiyar alQaidah ce ta ƙaddamar. Ɗaya daga cikin waɗanda kissar ta rutsa da shi dai harda shugaban ƙabilar Ashal. A makonnin da suka gabata ne dai 'yan ƙabilu da dama suka marawa dakarun gwamnati baya wajen farma mayaƙan ƙungiyar alQaidah, waɗanda a yanzu ke riƙe da iko a garuruwa daba daban. A farkon wannan shekarar ne gwamnatin shugaba Ali Abdallah Saleh na ƙasar Yemen, wanda a halin yanzu ke yin jiyya a ƙasar Saudiyya ta rasa iko a yankuna daban daban dake kudancin ƙasar. A halin da ake ciki kuma an sami ɓaraka a majalisar 'yan adawar ƙasar Yemen, wadda aka samar a ranar Larabar da ta gabata da nufin warware taƙaddamar dake tsakanin arewaci da kudancin ƙasar. Mambobin 'yan adawa 23 dake wakiltar yankin kudancin ƙasar inda ake haƙo man fetur ne suka janye wakilcin su bisa hujjar cewar ana nuna musu wariya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu