1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙabilanci a Libiya ya janyo asarar rayuka

March 27, 2012

Mummunan taho mu gama tsakanin ƙabilu a kudancin Libiya ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 30 yayin da dama suka ji raunuka.

ARCHIV - Libysche Rebellen schauen sich am 25.05.2011 ein bei Kämpfen zerstärtes Auto in Misrata an. Die Wunden, die der Krieg geschlagen hat, sind noch nicht verheilt. Trotzdem herrscht Aufbruchstimmung in Libyen - ein Jahr nach dem Beginn des Aufstandes gegen Gaddafi erfindet sich ein Volk neu. Foto: MISSAM SALEH dpa (zu dpa-KORR.: «Libyen ein Jahr danach - Ein Volk erfindet sich neu» vom 12.02.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Rigingimu a sassa daban daban na Libiya sun ƙi ci sun ƙi cinyewaHoto: picture alliance/dpa

Aƙalla mutane 30 aka kashe sannan sama da 100 aka ji wa rauni a cikin kwanaki biyu na wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a birnin Sabha dake kudancin ƙasar Libiya. Likitoci a yankin sun faɗa wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa waɗanda suka rasu 'yan ƙabilu ne dake yaƙar ƙabilar Toubou masu ɗaukar makami dake a birnin na yankin hamada mai nisan kilomita 750 kudu da Tripoli babban birnin ƙasar. Sai dai shugaban ƙabilar ta Toubou Issa Abdel Majid Mansur ya ce 'yan ƙabilarsa 40 aka kashe, kuma ya zargi mahukuntan Libiya da amfani da jiragen saman yaƙi da motocin sulke akan wuraren 'yan Toubou dake kudancin birnin na Sabha. Shugaban rundunar tsaron ƙasa a yankin, Kanal Mohammed Bussif ya ce ana cikin wani hali mai sarƙaƙƙiyya a yankin, inda ya zargi wasu ɓatagari dake samun goyon bayan ƙasashen ƙetare.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi