Rikicin addini a Kenya
June 8, 2007Talla
Wasu ƙarin mutane 11 sun rasa rayuka a ƙasar Kenya a sakamakon faɗan da ya ɓarke tsakanin jami´n tsaro, da wata ɗarika mai suna Mungiyi, da gwamnati ta haramta.
Gwamnatin Kenya, na zargin wannan ɗarika da ƙirƙiro saban addini, wanda ba a san kan digin sa ba, kazalika, memboni ta, sun yi ƙaurin suna wajen aikata kissan kai, a sassa daban-daban na ƙasar.
Rikici tsakanin yan sanda, da ƙungiyar Mungiki, ya fara tun ranar talata da ta wuce.
Mutane a ƙalla 22, su ka rasa rayuka a ranar farko.
Shugaban ƙasar Kenya Mwai Kibaki, da kan sa, ya gabatar da jawabi, inda ya umurci jami´n tsaro su fattaki membobin ƙungiyar Mungiki, muddun ba su bada kai, bori ya hau ba.