Rikicin addini a Masar
January 3, 2011![](https://static.dw.com/image/6380507_800.webp)
Shugabannin siyasa da na addini a nan Jamus sun yi kira ga gwamnatin Masar da ta ƙara ɗaukar matakan ba da kariya ga Kiristoci tsiraru a ƙasar. A jiya daddare an sake yin arangama tsakanin 'yan sanda da ɗaruruwan Kiristoci mabiya ɗarikar Coptic a Masar dake zanga-zangar yin tir da harin ƙunar baƙin wake da aka kai kan wani coci dake a birnin Alexandria a jajebaren ranar sabuwar shekara. Volker Kauder shugaban ɓangaren jam'iyar CDU a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ya ce ya kamata Jamus ta ƙara matsawa Masar lamba domin ta yaƙi masu tsattsauran ra'ayin addini. A kuma halin da ake ciki shugaban cocin Coptic a Jamus, Anba Damian ya ce 'yan sandan tarayya sun gargaɗe shi game da barazanar kai hare hare kan 'yan Coptic a Jamus a wannan wata.
"'Yan sandan tarayya sun yi gargaɗin cewa a intanet ana yaɗa wata maƙarƙashiya ta kaiwa majami'un Coptic a ƙasar harin ta'addanci daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Janeru wato ranar bikin Kirsmettin mu."
Cocin na Coptic ya bayyana wannan harin a Alexandria da cewa sakamakon ƙyamar da ake nuna musu da ya yawaita a watannin baya-bayan nan.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi