1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin addini a Masar

May 8, 2011

Gwamnatin Masar ta tsaurara matakan tsaro sakamakon ɓarkewar rikici tsakanin musulmai da Kristoci a birnin al-Ƙahira

Ma'aikatan kashe gobara a lokacin da suke kashe wutar da aka cunna wa cociHoto: picture-alliance/dpa

Majalisar ministocin Masar ta ce za ta tsaurara tsaron ƙasar kwana ɗaya bayan da aka yi arangama tsakanin Musulmai da Kristoci a birnin al-Ƙahira da mutane10 suka rasa rayukansu a cikinta. Sojoji sun killace wurin da wannan arangamar ta auku tare da yin harb-harbe domin tarwatsa taron jama'a. An kuma girke dakaru a kewayen coci coci da ke wannan wuri domin ba da kariya ga duk wani hari da masu matsanancin ra'ayi na islama ka iya kaiwa akan krisotoci. Wannan rikicin ya ɓarke ne bayan da ɗaruruwan Musulmai suka yi jerin gwano zuwa ginin wani coci da suka yi imanin cewa ana tsare da wata mata saboda musulunta da ta yi. Shugabannin mulkin sojan ƙasar ta Masar sun ce ko kafin wayewar gari an kame mutane 190 da ake zaton suna da hannu a wannan rikici. Za a kuma gurfanar da su a gaban kotun soji.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi