1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin APC lalacewar lamura ga masu mulkin Najeriya

October 25, 2016

Duk da cewar dai sun dauki lokaci suna kokarin danne zuciya tsakanin juna, daga dukkan alamu igiyar da ta daure tsintsiyar APC ta fara nuna alamar gajiya ko sako-sako.

Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Hoto: Chris Stein/AFP/Getty Images

A wani abun da ke zaman alamun lalacewar lamura a cikin jam'yyar APC mai mulki gwamnonin cikin gidan jam'iyyar da ma ragowar masu ruwa da tsakinta sun nemi sauyin tsari a cikin harka ta bada mukamai na gwamnatin ta Buhari in har ana da fatan kai wa ya zuwa tudun mun tsira a nan gaba.

Duk da cewar dai sun dauki lokaci suna kokarin danne zuciya tsakanin juna, daga dukkan alamu igiyar da ta daure tsintsiyar APC  ta fara nuna alamar gajiya tare da wani sabon rikici na neman barkewa a tsakanin manyan 'ya'yanta.

Wasu jerin sunaye na jakadu ne dai ya kai ga tada tsimi a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da suka ce tura ta  kai bango kuma hakurinsu ya kare da gwamnatin da ke kan mulki a Abuja.

Tuni dai Aisha Buhari ta ce ba da ita ba idan tafiyar ta ci gaba a hakaHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Gwamnonin jam'iyyar APC dai sun gana da shugaban kasar sun kuma ce akwai bukatar gyara da nufin ceton jam'iyyar da yanzu haka ke cikin wani yanayi mara kyau.

Owele Rochas Okorocha dai na zaman gwamna na jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC  kuma  a fadarsa  a raba kowa ya san nai kawai zai fitar da jam'iyyar daga korafin da ya yi nisa a tsakanin 'ya'yanta.

Simon Lalong dai na zaman gwamna a Plateau da kuma ya ce ba tsari yadda aka kai ga fitar da daukacin mukaman na Plateau daga yankin.

Hoto: DW/K. Gänsler

Rubutu da nufin gyara ko kuma kokari na tunkarar halaka dai jam'yyar ta shiga tsananin rudu sakamakon mataki na shugaban kasar na nadin daukacin mukamai na gwamnatin ba tare da tuntuba ga gwamnonin da ma ragowar masu ruwa da ma tsaki cikin harkokin sauyin ba.

To sai dai kuma in har gwamnonin na shirin su rubuta domin gyara dai alamu na nunin kai karshen hakurin 'ya'yan jam'iyar da tuni wasu suka fara karta kasar ko mutuwa ko yin rai a cikin tsarin na tsintsiya.