Rikicin bayan zaɓe a Mexico
July 8, 2012Dubun dubatan masu zanga-zanga suka fantsama kan titunan babban birnin Mexico ranar asabar domin nuna adawa da nasarar an takarar shugaban ƙasar Enrique Pena Nieto. Masu zanga-zangar na zargin cewa jamiyyar Pena Nieto ta Institutional Revolutionary Party wato PRI ta bayar da abinci kyauta, da katunan sayayya a manyan shaguna, da ma wasu mahimman kyautai masu ƙayatarwa ga jama'a, kafin zaɓen da aka gudanar ranar ɗaya ga watan Yuli.
Hukumar zaɓen Mexico to riga ta tabbatar da nasarar Peno Nieto tun ranar juma'ar da ta gabata, inda ta bayyana cewa ratar kashi bakwai cikin 100 ne ke tsakaninsa da abokin hammayarsa Andres Manuel Lopez Obrador. Wannan nasara ta Nieto ya maido mulki ga jamiyyar ta PRI wacce ta yi mulki a ƙasar na tsawon shekaru 70 kafin ta sha kaye a shekarar 2000 bayan da aka yi ta zarginta da murɗiyyar zaɓe da mulkin danniya.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal