1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin bayan zabe a Tanzaniya ya yi kamari

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 31, 2025

Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan Adam na nuna damuwa kan halin da ake ciki a kasar Tanzaniya

Zanga zangar bayan zabe a kasar Tanzaniya
Zanga zangar bayan zabe a kasar TanzaniyaHoto: AP Photo/picture alliance

Ana dai ganin Shugaba Samia Suluhu Hassan da ke neman tazarce, na amfani da karfin iko wajen murkushe 'yan adawa. 

Al'ummar ta Tanzaniya dai sun fantsama kan tituna, inda suke zanga-zangar adawa da sakamakon zaben da ke nuni da yiwuwar cewa Shugaba Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 29 ga wannan wata na Oktoba.

Rahotanni sun nunar da cewa kimanin mutane 700 ne suka halaka, a yunkurin jami'an tsaro na murkushe masu zanga-zangar da karfin tuwo kamar yadda babbar jam'iyyar adawa ta Chadema ta yi zargi.

Karin Bayani: 'Yan adawa na fargabar salon mulkin danniya a Tanzaniya

Zanga zangar bayan zabe a kasar TanzaniyaHoto: AP Photo/picture alliance

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a kiyaye rayukan al'umma, tare kuma da yin kira ga jami'an tsaro da su guji amfani da karfin da ya wuce kima. Kakakin Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniyar Seif Magango ne ya yi wannan kiran a yayin taron manema labarai a Geneva, inda ya kara da cewa:

"Muna bukatar mahukuntan Tanzaniya da su tabbatar da yin bincike ba tare da nuna wariya ba, a kan duk wani hargisti da ke da alaka da zabe tare da tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu."

Da yake karin haske kan halin da ake ciki, Roland Ebole da ke yi wa kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International bincike a yankin a kasashen Tanzaniya da Yuganda ya bayyana cewa abokan huldarsu da ke Tanzaniya sun tabbatar musu da ganin gawarwakin jama'a birjik a kan tituna.

Karin Bayani: Tanzaniya: Zabe ba tare da 'yan adawa ba

Zanga zangar bayan zabe a kasar TanzaniyaHoto: AP Photo/picture alliance

A cewarsa babu gaskiya a adadin da ake sanarwa na mutanen da suka halaka daga mahukunta, inda ya ce suna kokari ne su nuna abin bai kai yadda ake tsammaninsa ba. Da yake jawabi kan matsayar da Shugaba Suluhu Hassan ta dauka kuwa cewa ya yi:

"A wannan zaben da Samia Suluhu Hassan ta aiwatar da duk alkawuran da ta dauka lokacin da take kan mulki ba tare da ta yi tunanin lashe zabe bayan ta kammala wa'adinta na farko ba, duk da cewa ba zabe ne ya kawo ta kan mulki ba ta gaji shugaban kasa John Magafuli ne bayan mutuwarsa, a yanzu za ta iya lashe zaben cikin sauki ta hanyar janyo wa kanta farin jini. Ko kuma da ko za ta fadi a zabe da ta tsira da kimarta da mutuncinta, saboda ta yi abin da ya dace ga al'ummar Tanzaniya."

Tuni dai mahukuntan suka musanta yin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar, inda a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al-Jazeera ministan harkokin kasashen ketare na Tanzaniyan Mahmoud Thabit Kombo ya nunar da cewa, ba su da wani adadi na mutanen da suka halaka. Akwai kyakkyawan fatan samun sauye-sauye da gudanar da zabuka masu inganci, yayin da Shugaba Suluhu Hassan ta karbi madafun iko bayan mutuwar Shugaba John Magafuli ta takasance mataimakiyarsa kafin rasuwar tasa a shekara ta 2021.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW