1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Burma

September 26, 2007

Ayayinda komitin sulhu na mdd ke shirin gudanar da taro na musamman adangane da halin da ake ciki a kasar Burma,ko kuma Myammar,rahotanni na nuni dacewa jamian tsaro sun bindige biyar daga cikin masu zanga zangar adaw da gwamnati a babban birnin kasar dake Rangoon.Bugu da kari an cafke akalla mutane 200,ayayinda ake cigaba da harbin barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu boren,wadanda sukayi watsi da umurnin gwamnati na zama a cikin gidajensu.Wadanda suka ganewa idanunsu wannan rikici,sun shaidar dacewa jamian tsaro na cigaba da dukan sanannun malaman addinin Bhuda da ake darajawa a kasar ta Burma,tare da durasu acikin motoci domin tafiya dasu wurin da zaa tsare su.Ayau ne dai aka shiga yini na tara a jere ana wannan zanga zangan adawa da gwamnatin sojin wannan kasa ,wanda ke zama mafi munin irinsa a shekaru 20 da suka gaba a wannan kasa.