Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya
November 4, 2013A wani abun dake zaman alamu na irin rikicin da ke gaba a tsakanin fadar gwamantin tarrayar Najeriya da kuma 'yan bakwai na sabuwar PDP, 'yan sanda sun mamaye taron 'yan bakwan cikin daren wannan Lahadi (03. 11.13) a Abuja.
Alamun rikicin dai ya faro ne lokacin da babban jami'in 'yan sandan da ke kula da yankin Asokoro a nan Abuja, ya kutsa kai gidan gwamnatin Kano a Abujar, ya kuma shaidawa wasu gwamnoni biyar na sabuwar PDP da ragowar manyan shugabannin jam'iyyar na kasa cewar fa taron nasu na zaman na haramun, ya kuma sabawa ka'ida.
Jami'in da ke samun rakiyar wasu motocin 'yan sanda guda uku dauke da makamai dai, yace yana da umarnin babban sufeton 'yan sanda na kasa na tarwatsa taron da ke zaman irinsa na farko tun bayan fara taruka da 'yan jam'iyyar APC.
Takaddama a tsakanin jami'an tsaron Najeriya
To sai dai kuma an kai ga yin cirko cirko dama daga jijiyar wuya a tsakanin jami'an tsaron gwamnonin da suka nemi yi wa dan uwan nasu kora ta kare, da kuma nasa 'yan sandan da suka ce cika umarnin magabata na zaman wajibi a garesu.
Tsoma bakin gwamnonin da suka tsaida taron nasu suka kuma gayyaci jami'in dan sandan, sannan suka shaida masa basu da niyyar bin umarnin nasa dai, ya tilasta 'yan aiken komawa gefe, tare da kyale ci gaba da kammala taron.
To sai dai kuma an kammalashi tare da bacin rai a tsakanin gwamnonin da suka kira matakin jami'an tsaron raini na hankali dama kokari na kyeta rigar 'yanci, a cewar Sule Lamido da ke zaman gwamnan jihar Jigawa, kuma daya daga cikin mahalarta taron.
Sabuwar PDP ta yi Allah wadai da kutsen gwamnati
Akalla sau dai dai har uku ne dai jami'an tsaron kasar suke kokarin hana taruka na sabuwar PDP cikin tsawon makonni ukun da suka gabata, a wani abin da ke zaman alamu na karshen hakurin mahukuntan kasar ta Najeriya, da ke nuna alamun hadawa da karfi na hatsi da nufin kawo karshen ayyukan na sabuwar PDP, da sannu a hankali ke karkata ya zuwa ga adawa.
To sai dai kuma a Fadar gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso da ya sauke bakin na daren wannan Lahadin (03.11.13) dai, mamayar 'yan sandan ba wai kawai taka hakki na 'yan bakwai na PDP ne ba, amma yana zaman keta mutuncin mutan Kano da ke da mallakin gidan na Abuja, da kuma gwamnoni ke shirin bata muhimmancin da ya dace da ita.
Kowane lokaci cikin makon nan ne dai, ake sa ran komawa bisa teburi na shawara a tsakanin fadar shugaban kasar, da gwamnonin da suka share kusan daukacin makon jiya suna ganawa da jami'an jam'iyyar APC ta adawa.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh