1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Takun saka a tsakanin China da Japan na kara kamari

November 19, 2025

Rikicin diflomasiyya a tsakanin China da Japan ya dauki sabon salo tare da yin barazana kan huldar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Firaministar Japan Sanae Takaichi da shugaban China Xi Jinping
Firaministar Japan Sanae Takaichi da shugaban China Xi JinpingHoto: Japan Pool/Jiji Press/AFP

Kafafen yada labarai na Japan sun ruwaito cewa a wannan Laraba China za ta dakatar da shigo da kaya ta Tekun Japan, yayin da kasashen biyu suka bude babin takun sakar diflomasiyya, sakamakon kalaman firaministar Japan kan tsibirin Taiwan da China ke ikirarin wani yanki ne na kasarta.

Takun sakar ya samo asali ne tun a ranar bakwai ga watan Nowamba, bayan da firaministar Japan Sanae Takaichi ta furta cewa idan har China ta yi kuskuren daukar matakin soji a kan Taiwan, Japan za ta samu hujjar tura sojojinta domin kare tsibirin a karkashin wata dokar kasar da aka amince da ita a 2015, lamarin da bai yi wa Beijing dadi ba.

Kamarin takun sakar ya kai Beijing ga kiran 'yan kasarta da su dakatar da tafiye-tafiye zuwa Japan, yayin da fadar mulki ta Tokyo ta bukaci 'yan kasarta da ke China da su yi taka-tsantsan

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da da kyar da jibin goshi China ta dawo da alakar cinikayya a tsakaninta da Japan tun bayan takunkumi da aka labta wa fadar mulki ta Tokyo saboda sakin gurbataccen ruwa na kokara daga lalatattar cibiyar makamashi ta Fukushima a 2023.