1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Neman mafita ga makiyaya

February 10, 2021

A yayin da ake ci gaba da neman mafitar rikicin makiyaya da manoma, hankali yana ta karkata a zuciyar mahukuntan Najeriya na kare tsarin kiwon gargajiyar shekaru aru-aru a kasar.

Nigreria Fulani-Nomaden
Yaran Fulani makiyaya ba sa samun damar zuwa makaranta sakamakon yawon kiwoHoto: AFP/Luis Tato

Ra'ayi dai daga dukkan alamu yana zuwa daya, a tsakanin shugabanin a Najeriyar, walau a sashen kudancin ko na arewaci, game da kare batun kiwon dabbobbi na al'ada. Wani taron gwamnonin arewacin kasar dai, ya bi sahun 'yan uwansa da ke kudanci wajen yanke hukuncin cewar kai kawon shanu da Fulanin ba zai  dore a cikinNajeriyar ba, kasar da ke kallon karuwar tayar da hankali sakamakon rikicin makiyaya da manoma da kuma siyasar da ta mamaye shi a yanzu.

Karin Bayani: Fulani makiyaya cikin fargaba

Gwamnonin dai sun ce dole masu sana'ar kiwon su rungumi ajiye shanun wuri guda, domin kai karshen gwagwarmaya ta mallakar filayen noma ko kuma burtulai da ta rikide zuwa barazanar tsaron kasar mai girma. Tun kafin yanzu dai, jihohi da daman gaske sun kai ga ware daruruwan miliyoyin Nairori da sunan sake tsugunar da masu sana'ar kiwon da ke zaman masu sana'a daya tilo da babu tallafin gwamnati cikin sana'ar tasu.

Gwamnonin arewacin Najeriya sun bi sawun gwamnan jihar Kano Umar Abdullahi GandujeHoto: Abdulkareem Baba Aminu/DW

Sama da Naira miliyan dubu 350 ne dai alal ga misali, babban bankin kasar CBN da ma ragowar gwamnatoci suka kai ga batarwa wajen habaka harkar noma, a yayin kuma da babu ko silai ga masu sana'ar kiwon ko dai da nufin tsugunar da Fulanin ko kuma inganta sana'ar zuwa ta zamani. Abun kuma da a cewar Usman Baba da ke zaman sakataren kungiyar Fulani ta kasar, ake bukatar da a sauya cikin matakan sake zaunar da su domin cin gajiyar san'ar kiwo a kasar.

Karin Bayani: Cimma yarjejeniyar sulhu da makiyaya

To sai dai koma ya zuwa ina masu mulki na kasar suke shirin zuwa da nufin jan aikin tsugunar da Fulanin dai, a baya wasu a cikin jihohin sun yi nasarar samun tsarin da ya hada manoman da makiyayan ba tare da samun rikici ba. Kuma a fadar Isa Tafida Mafindi da ke sana'ar noman da kiwo, jihar Kano can baya tai nasarar hade masu sana'ar kiwon da noman a cikin wani tsarin  da ke da ban mamaki. Najeriyar dai na da shanu kimanin miliyan 20 da ke gararamba, ko bayan na makwabtan ksashen yankin yammacin Afirka da ke kai kawo  a cikin kasar da zummar inganta rayuwar dabbobbin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani