Rikicin gabacin Kongo ya dauki sabon salo
August 30, 2013Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda a babban labarinta mai taken gumurzu mai hadari ta mayar da hankali a kan Kongo tana mai cewa ba hare-haren sojojin Majalisar Dinkin Duniya a kan 'yan tawaye kadai ke karuwa ba, a'a ana kuma kai farmaki na bindigogi atileri a tsallaken kan iyaka, inda rayuka suka salwanta a Ruwanda sannan sai ta ci gaba kamar haka.
"Wannan shi ne fada mafi muni da aka fuskanta a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo cikin shekaru da dama. Da alikoftocin yaki na kasar Ukrain da bindigogin atileri na kasar Tanzaniya da sojojin kundun bala na Afirka ta Kudu tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Kongo wato Manusco ta taimaka wa sojojin kasa na Kongo a farmakin da suka kai wa 'yan tawayen kungiyar M23 a birnin Goma. An kashe sojan Tanzaniya daya sannan wani sojan Afirka ta Kudu ya samu rauni, amma ba wanda ya kirga sojojin Kongo da fadan ya rutsa da su. A karon farko cikin wannan rikici an samu salwantar rayuka da wadanda suka jikkata a garin Gisenyi dake bangaren Ruwanda na kan iyakar kasashen biyu. Sannan su kuma sojojin Kongo sun sanar ta shafin intanet cewa a hukumance yanzu Ruwanda ta kutsa cikin Kongon don tallafa wa kungiyar M23. Sai dai mazauna a Goma ba su tabbatar da wannan zargi ba. Yanzu haka yankin kan iyakar ya zama wani fagen daga inda gwamnatocin Kongo da Ruwanda ke zargin juna da laifin tabarbaewar halin da ake ciki."
Zabe ka iya guba ga demokradiyya
Ita kuwa a sharhinta jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi game da zabe da kuma damokradiyya a Afirka tana mai cewa a wasu lokutan zabuka ka iya zama guba ga tsarin demokradiyya, domin ana samun yawan kasashen Afirka Kudu da Sahara dake gudanar da zabuka amma sau tari wadannan zabuka na kara rura wutar rikice-rikice ne maimakon maganinsu.
"A bayan nan an gudanar da muhimman zabuka a kasashe biyu. Na farko a Mali mai fama da rikici sai kuma a Zimbabwe. Yayin da aka kwatanta zaben Mali da cewa yayi nasara, amma an tabka magudi lokacin sake zaben shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe. Ko dai wani hali ne ake ciki, a cikin shekarun baya bayan nan dai yankin Afirka Kudu da Sahara na kara zama wani yanki mai shirya zabuka ta bin tsarin demokradiyya. Sai dai duk da haka zabuka kadai ba sa nufin demokradiyyar ta wanzu musamman idan manufar demokradiyya ta wuce wani tsarin mulki na masu rinjaye a kan marasa rinjaye. A da yawa daga cikin kasashen Afirka da ake yawaita gudanar da zabe ana kwan gaba kwan baya tsakanin demokradiyya da mulkin kama karya. Wasu lokutan zabuka a kasashen rikici suke haddasawa saboda fatali da hakkin jama'a."
Rashin sanin tabbas ga makomar dalibai
Daliban Laberiya ba su cancanci shiga jami'a ba inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai cewa fatan samun karin ilimi ga dalibai dubu 25 dake da niyar shiga jami'a a Laberiya ya gushe tun kafin ma su fara. Domin dukkansu sun fadi jarrabawar neman shiga jami'ar kasar. Ministar ilimin kasar da ta bayanna wannan faduwar daliban da wani kisan kare dangi da aka yi wa ilimi, ta ce za ta shiga tattaunawa da jami'ar don samun mafita.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu