1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Gadhafi da 'yan tawayen Libiya

May 12, 2011

Bama-bamai sun yi ta fahewa a Tripoli na Libiya bayan fitowar shugaba Gadhafi ta tshar telebijin

Wani gida a Misrata bayan harin makamai a ranar 23. 04. 2011.Hoto: AP

Rahotannin dake fitowa daga Libiya sun nuna jin ƙarar tashin bama-bamai a sassa daban daban na Tripoli, babban birnin ƙasar cikin dare. Hakanan wakilan kafofin yaɗa labarai sun ruwaito jin ƙarar jiragen saman yaƙi dake yin shawagi a sararin samaniyar birnin. Wannan yana zuwa ne sa'oi ƙalilan bayan da shugaba Moammar Gadhafi na ƙasar ya yi bayyanar sa ta farko ta tashar telebijin cikin kusan makonni biyun da suka gabata.

Hotunan telebijin ɗin dai sun nuna shugaban na Libiya na ganawa da wasu mutanen da tashar telebijin ta ƙasar ta ce shugabannin ƙabilu ne. Idan za'a iya tunawa dai ba'a sake ganin shugaban na Libiya ba tun bayan wani harin da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta ƙaddamar a ranar 30 ga watan Afrilun daya gabata, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar ɗan shugaba Gadhafi da kuma wasu jikokin sa uku.

A halin da ake ciki kuma 'yan tawayen ƙasar ta Libiya sun yi da'awar sake karɓe iko da babban filin saukar jiragen saman birnin Misrata bayan arangamar da suka yi da dakarun gwamnati.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar