Takon saƙo a game da cinikiyar Gaz
January 4, 2009A wannan karo shirin ciniki da masana´antuzai duba rikicin da ya ɓarke tsakanin Russia da Ukraine a game da cinikiyar iskan Gaz wanda kuma ya shafi wasu ƙasashen Turai.
Ranar 23 ga wartan Desember na shekara bara, ƙasashen da suka mallaki albarkatun iskan Gaz, wanda suka haɗa da Russia, Iran , Qatar Venezuela ,da Algeria, suka kamalla zaman taro a birnin Mosko, inda suka yanke shawara girka wata Ƙungiyar ƙasashen masu arzikin iskan Gaz.
A yayin da yake jawabin bude taro Firamninistan kasar Russia Vladmir Poutine ya bayyana cewar lokacin arhar iskan Gaz ya ƙaura.
Ƙasa da sati guda bayan wannan huruci, ƙasar Russia ta buƙaci ƙara farashen Iskan Gaz da take sayarwa UKraine da kashi kussan 30 cikin ɗari.
A wani mataki mai kama da kora da hali, hukumomin Kremblin suka ce ba za su rattanaba hanu akan warta sabuwar yarjejiyar ba da takwarorinsu na KIev har sai sunbiya tsabar bashin da aka tambayo su na Gaz ɗin da suka sha baya ,wanda yawan shi ya tashi dalla Amurika miliyan dubu biyu da kusanrabi,kuma kamin 31 ga watan Desember.
Bayan tattanawar da suka yi tawagogin ƙasashen biyu, sun kasa cimma yarjejeniya, kamar yadda shugaban kamfafin Gazprom na Russia Alexei Miller ya nunar:Tattanawa tsakanin mu da Ukraine a game da batun Gaz a shekara ta 2009 ta cije.
Ya zuwa yanzu, Gazprom bai samu ko ƙwandala daga Ukraine ba, kuma ba za mu amincewa da alƙawura na fatar baka ba.
Munyi imanin cewar, hukumomin Ukraine na buƙatar shiga rikici tare da mu.
Bayan watsewar da aka yi barambaram,a taron ƙarshe da ya haɗa wakilan ƙasashen Ukraine da na Russia Firaminista Vladmir Poutine yayi barazanar yanke Gaz ga wannan ƙasa tare da cewa:
Idan Ukraine ta kasa cika alƙawarin da ta ɗauka na biyan bassusukan da muka tambayo ta, ko mi ya biwo baya itace ce sanadiya.
Abin da ya biwo bayan jim kaɗan bayan bayyanin Vladmir Poutine shine tsinkewar bututu dake jigilar Gaz daga Russia zuwa Ukraine, a ƙarfe bakwai na ranar 1 ga watan Janairu shekara ta 2009.
Gwammnatin Ukraine ta bayyana matuƙar mamaki da ɓacin rai ga wannan mataki.
Hujjojin da suka bada na kasa biyan bashin da Russia ta tambayo su, sun haɗa da matsalolin hada hadar kuɗaɗe da suka shafi dukkan ƙasashen duniya.
A game da ƙarin farashen Gaz kuma sun gitta sharaɗin sai Russia ta ƙara farashen kuɗin da take biyan Ukraine na jigilar iskan zuwa ƙasashen turai kamar yadda shugaban ƙasar Ukraine Viktor Ioutchenko ya nunar:
Russia ta yanke hukunci hauda farashen gaz da take saida mana, da kashi 30 cikin ɗari, wato akan dalla 250 duk lita dubu.
Mun yi watsi da wannan farashe, kuma mun buƙaci itama Russia ta ƙara farashen da take biyan Ukraine na jiggilar Gaz da muke mata zuwa ƙasashenTurai da kashi 30 cikin ɗari, ta ƙi amincewa da wannan ƙari.
Shugaba Ioutchenko, ya dangata rikicin Gaz da Russia a matsayin wani mataki na a laɓe ga guzuma domin a harbi karsa.
A cewar sa, Russia ta yanke wannan shawara badan komai ba, face ta nuna adawa, a game da yada ƙasar Ukraine dake ƙarƙashinTarayya Soviet a baya, ta juya akalar ma´amilarta da ƙasashen turai tun zamanin juyin juya halin shekara ta 2004.
Mafi yawa daga iskan Gaz da Russia ke saidawa ƙasashen turai na bi ta ƙasar Ukraine, ta hanyar bututu dabam dabam da kamfanin Gazprom ya shinfiɗa cikin ƙasar.
To saidai ƙasashen biyu sun yi kira ga sauran ƙasashen turai su kwantar da hankali domin rikicin bai zai shafe su ba.
Amma kwana biyu bayan katsewa Ukraine bututun dake shayar da ita Gaz, hukumomin Russia sun zarge ta, da sace wani sashe na Gaz dake zuwa wasu ƙasashen turai kamar inji shugaban kafanin Gazprom Alexei Miler:
Mun gano raguwa iskan Gaz dake zuwa ƙasashen Turai , mussamman Hongrie ,Slovakiya, Roumaniya da Poland.
saboda haka, tunni mun fara duba sabin hanyoyin jigigilar Gaz zuwa wannan ƙasashe.
Kamfanin Gaz ya bayyana aniyar gurfanar da Ukraine gaban kotun ƙasa da ƙasa mai kula da shari´ar makamashi dake birnin Stohkolm na ƙasar Sweeden, ta la´akari da yadda a cewar Kamfanin Gazprom Ukraine ta taka dokokin ƙasa da ƙasa na jigilar iskan Gaz daga wata ƙasa zuwa wata.
Ba da wata wata ba, kamfanin gaz na ƙasar Ukraine Naftogaz ya mussanta wannan zargi ,tare da tuhumar Russia da rage yawan gaz ɗin da ganga da nufin ɓata sunan ƙasar Ukraine.
Rikicin dake wakana tsakanin Russia da Ukraine a game da Gaz na tada hankalin ƙasashen turai, domin kashi ɗaya cikin huɗu na Gaz da ake anfani da shi a ƙasashe dabam dabam na turai na zuwa daga Russia ta hanyar bututun dake rastawa a Ukraine.
A game da haka, kakakin gwamnatin ƙasar Jamus Thomas Steg, yayi kira ga ƙasashen biyu su kiyaye abunda zai sa rikicin ya ɓulla ga sauran ƙasashe:
ya zama wajibi ga Russia da Ukraine su ɗauki dukkan matakan da suka dace ,don keɓe ƙasashen Turai gada wannan taƙƙadama.
Mu dai a Jamus, ya zuwa wannan lokaci bamu da fargaba a game da iskan Gaz.
kakakin ministan Jamus dake kulla da makamashi Beatrix Brodkorb ta bayana yawan Gaz da kasar ta mallaka:
Tankunanmu na tsimin Gaz shaƙe suke, sabo hada bamu da wata fargaba.
Muna da a ƙalla kashi 25 cikin ɗari na buƙatarmu ta Gaz a cikin shekara.
Kashi 37 cikin ɗari na Gaz ɗin da ake amfani da shi a nan ƙasar Jamus na zuwa daga Russia.
Sannan hukumar makamashi ta ƙasa, na odar sauran buƙatocin ƙasa na Gaz daga ƙasashe kamar su Nowe, Holland, Danmark da Engla.
Jamhuriya Tcheque dake matsayuin jagorar Ƙungviyar Tarayya Turai a halin yanzu, ta yi kira ga hukumomin Mosko da na Kiev, su himmantu domin kawo ƙarshen wannan rikici, wanda ba shi bane na farko.
Cemma a shekara ta 2006 irin wannan rikici ya faru ,wanda kuma bayan Ukraine ya shafi dukan ƙasashen turai ,wanda suka yi dogaro da iskan Gaz daga Russia.
Bayan yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka cimma a watan Oktober na shekara ta 2007, sun sake shiga wata sabuwar badaƙƙala a watan Maris na shekara da ta gabata, bayan da Russia da rage yawan Gaz da take baiwa Ukraine da kashi 50 cikin ɗari.