1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin gidan yari ya yi ajalin fursunoni a kasar Ecuador

Abdoulaye Mamane Amadou
September 25, 2025

Fursunoni masu fada da juna sun yi mummunan fadan da ya yi sanadin mutuwar mutane 17 a yankin Esmeraldas na arewacin kasar Ecuador

Hoto: Jonathan Miranda/EPA

Wasu fursunoni masu hamayya da juna sun yi bai wa hamatta iska a gidan yarin Esmeraldas, daf da iyakar kasar Colombia daga yankin arewaci. Jami'ai sun ruwaito cewar fadan na wannan Alhamis, ya yi musabbabin ajalin akalla mutane 17, kamar yadda rundunar 'yansandan kasar ta tabbatar.

An samu karuwar aikata laifukan kisa a kasar Ecuador

Ko a ranar Litinin din da ta gabata ma dai sai da wani rikici a tsakanin gungun masu fada da juna ya kai ga kashe fursunoni 13 da gandiroba guda  a wani gidan yari na yankin Macahala na kudu maso yammaci

Fursononin Ecuador sun yi garkuwa da gandurobobi

Hotuna da aka yada a kafafen sada zumunta, kana aka tabbatar da sahihancinsu, sun nuna wasu maza kwance a kasa, ba riga a jikinsu, jini na kwarara, ciki har da biyu da aka fillewa kai.

Gidajen yari a kasar Ecuador dai sun cika sun batse, kana sun zama wasu cibiyoyi da kungiyoyin masu aikata laifuka ke fakewa da su suna kara aikata barna.