1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rikicin gwamnatin Jamus riba ga AfD

Mouhamadou Awal Balarabe
November 8, 2024

A Jamus, jam'iyyar AfD mai kyamar baki ta sabunta kiran da ta dade tana yi na a gaggauta gudanar da sabon zabe bayan da kawance Jam'iyyun da ke mulki ya ruguje. Wanna mataki na iya ba ta damar samun karin kuri'u

Bundestag Plenardebatte |  Jüdisches Leben in Deutschland
Hoto: Christophe Gateau/dpa/picture alliance

Tun bayan da kawancen jam'iyyu uku na SPD da Greens da FDP suka hada gwiwa wajen kafa gwamnatin tarayyar Jamus a karshen watan Disamba 2021, jam'iyyar AfD take kakkausar suka kan manufofin da suka sa a gaba. Alternative für Deutschland AfD ta zargi gwamnatin da Olaf Scholz ke jagoranta da gazawa a dukkan bangarorin siyasa, inda ta yi kira da a yi sauyin alkibla musamman a fannin shige da ficen baki da manufofin ketare.

Karin Bayani: Rikicin siyasa ya kunno kai a gwamnatin Jamus

Kamar zababben shugaban Amurka na 47 Donald Trump, Jam'iyyar na kan gaba wajen yaki da shigowar baki cikin Jamus ba bisa ka'ida ba da kuma manufar bude kan iyakokin kasar. Sannan Jam'iyyar ta AfD tana adawa da duk wani mataki na taimaka wa Ukraine da makamai, inda 'ya'yan jam'iyyar suka ki halartar zaman majalisa lokacin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi jawabi a majalisar dokokin Jamus Bundestag a watan Yunin 2024

Hoto: dts-Agentur/picture alliance

Don ganin cewar ta amfana da rikicin siyasa da gwamnatin tarayyar Jamus ta samu kanta a ciki ne, jam'iyyar AfD ta bukaci shugaban gwamnati Olaf Scholz ya amince majalisar dokoki ta Bundestag ta kada kuri'ar yankar kauna a ranar 10 ga watan Nuwamban 2024, maimakon watan Janairu kamar yadda ya bukata. Daya daga cikin shugabannin jam'iyyar AfD, Alice Weidel, ta ce wannan mataki zai sa a samu gwamnatin da za ta tsaya da kafafunta.

Karin Bayani: Barakar gwamnatin kawancen Jamus ta janyo cire ministan kudi

"Shugaba gwamnati Scholz ya dade da rasa amincewar al'ummar Jamus, don haka dole ne ya share hanyar gudanar da sabon zabe cikin gaggawa. Jam'iyyar AfD ta yi kira da a kada kuri'ar yankar kauna a farkon mako mai zuwa. Yana bin wannan kasa bashi, na gaggauta sauka daga mulki."

Hoto: Bernd Elmenthaler/Geisler-Fotopress/picture alliance

Ko shakka babu, sabbin zabukan da za a gudanar a Jamus na iya kara tasirin AfD a siyasar kasar. A zabukan tarayya da suka gudana a Satumban 2021, jam'iyyar da ke kyamar baki ta samu kashi 10% na kuri'un da aka kada. Sannan, kididdigar jin ra'ayin jama'a na Nuwamba 2024 ta nuna cewar kashi 17% na Jamsuwa na niyyar kada mata kuri'a. shugabannin jam'iyyar AfD sun nuna cewa a yakin neman zabe mai zuwa, za su ci gaba da mai da hankali kan batutuwan da suka shafi mafaka da matsalar bakin haure, da ke zama manufofin da suka dogara a kai tsawon shekaru a fagen siyasar Jamus. Ko da daya daga cikin shugaban AfD,Tino Chrupalla, sai da ya nemi a ci gaba da korar wadanda suka shigo Jamus ba bisa ka'ida ba.

Karin Bayani: Ana neman mafita ga tattalin arzikin Jamus

"Muna bukatar kawar da abubuwan da ke haifar da hijira ba bisa ka'ida ba a cikin tsarin zamantakewa. Muna son ganin fa'idoji na zahiri maimakon shafar mai a baka kamar yadda aka saba. Mu mayar da masu aikata laifuka kasashensu na asali tare da korar bakin da ba a amince da takardunsu na neman mafaka ba. Sannan, akwai bukatar rufe iyakoki tare da ficewa daga tsarin mafaka na EU, kamar yadda kasashe makwabta irin su Poland da Holland da Hungari suka riga sun nuna hanya."

Hoto: Markus Schreiber/AP/picture alliance

Domin aiwatar da manufofinta, jam'iyyar AfD na tallata manufar hadin gwiwa a fannin siyasa da jam'iyyun CDU da CSU da FDP don kafa gwamnatin hadin gwiwa, inda ta fi matsa lamba a kan jam'iyyar CDU da ke da ra'ayin rikau kuma ke bin manufofin jari hujja kamar ita. Sai dai da alama kawance tsakanin AfD da CDU bai zai samu ba, saboda jam'iyyar AfD ta kara tsattsauran ra'ayinta tun bayan zaben tarayya da ya gabata, lamarin da ya sa kotun kare kundin tsarin mulki Jamus ta ba da umurnin sanya ido a kan shugabanninta saboda tsauraran manufofinsu.

Wannan tsattsauran ra'ayi na AfD ne, ya sa shugaban jam'iyyar CDU Friedrich Merz da zai tsaya takarar shugabancin gwamnatin Jamus, ya bayyana a wata hira da rukunin kafofin yada labarai na kasar a watan Agustan 2024 cewar: "Ba za su iya yin aiki da wannan jam'iyyar ba, saboda zai kashe jam'iyyar CDU.