1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin gwamnatin Libiya da 'yan tawaye

May 9, 2011

NATO ta ce lokaci yana ƙurewa Gaddhafi a fafatawar da sojojin sa ke yi da dakarun ƙungiyar

Babban sakataren NATO Anders Fogh Rasmussen a tsakiya, yayin wani taron da ƙungiyar ta yiHoto: AP

Babban sakataren ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rusmussen ya faɗi - a wannan Litinin cewar, lokaci ya fara ƙurewa shugaban Libiya Muammar Gaddhafi a fito - na - fiton da dakarun sa ke yi da 'yan tawayen ƙasar waɗanda ke samun tallafin dakarun ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO. Babban jami'in na ƙungiyar NATO ya furta wannan kalamin ne duk kuwa da cewar dakarun dake goyon bayan shugaban na Libiya suna ci gaba da yiwa tashar jiragen ruwan birnin Misrata ƙawanya. Birnin dai na daga cikin yankuna - 'yan ƙalilan dake hannun 'yan tawayen a yankin yammacin ƙasar, wanda ke ƙarƙashin ikon shugaba Gaddhafi.

A halin da ake ciki kuma ƙungiyar agaji ta Red Cross ta isar da kayayyakin agaji kama daga abinci zuwa na kula da lafiya - ta hanyar jirgin ruwa ya zuwa birnin na Misrata a wannan Litinin, bayan da 'yan tawayen suka ce mazauna birnin na da abinci da ruwan da zai wadace su na tsawon wata guda ne kawai. Ƙungiyar ta Red Cross ta kuma bayyana taƙaicin ta game da zargin cewar dakarun dake biyayya ga Gaddhafi sunyi amfani da jiragen sama dake ɗauke da tambarin ƙungiyar wajen jefa nakiyoyi a tashar jiragen ruwan birnin Misrata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar