1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Irak

November 15, 2006

Pramninistan ƙasar Irak, Nuri Al Maliki ,ya umurci jami´an tsaro, su shiga farautar yan ƙunar baƙin waken da su ka sace wasu mutane, jiya, a birnin Bagadaza da rana gatse-gatse.

Wannan al´amari, mai ban mamaki, ya nunar da cewa, ko shakka babu, akwai hannun jami´an tsaron Irak, a hare haren da ake kaiwa wannan ƙasa.

Binciken da wasu daga cikin su ke gudanarwa, tamkar a yi sata da su ne, a kuma koma bin sau tare da su inji Nuri Al-Maliki.

A ranar yau laraba, yan takifen, su sako mutane fiye da 20, amma har yanzu, akwai sauran wasu cikin hanun su.

A yayin daya ke bayani da yan jarida, Praministan Irak, ya nuna matuƙar damuwa ga halin da ƙasar Irak ta tsinci kanta a halin yanzu.

A dangane da wannan rikici da ke ɗaiɗaita Irak, Majalisar Dokin ƙasar Russia, ta hiddo wata sanarwa a yau laraba , inda ta ce hukunci kissan da a ka yankewa tsofan shugaban ƙasa Saddam Hussain, zai zama wata sabuwar kafa ta ƙara durmuya Irak, cikin halin ni yasu, a game da haka, Majalisar Duma, ta yi kira ga kotuna da magabatan Irak, su ɗauki matakin hana zartar da wannan hukunci.