1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa

March 22, 2011

Rikici ya sake kunno kai a tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa dake mulki a zirin Gaza

Dakarun Hamas a wani ginin da Isra'il ta lalata ranar 19. 03.2011 a zirin Gaza.Hoto: picture-alliance/dpa

Jiragen yaƙin sojin Isra'ila sun ƙaddamar da samame a zirin Gaza bayan da mayaƙan sa kai na Falasɗinawa suka harba rokoki a kudancin ita Isra'ilar a ƙarshen mako. Jami'an kula da lafiya na Falasɗinawa suka ce samamen na Isra'ila ya haddasa rauni ga mutane 17 ciki harda ƙananan yara bakwai. Wani kakakin sojin Isra'ila ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar jiragen yaƙin na son lalata wasu abubuwa shida ne, waɗanda suka haɗa da wasu kayayyaki biyun da ake amfani da su wajen har-haɗa makamai, kana da hanyar ƙarƙashin ƙasa guda biyun dake da nufin kaiwa ga shingen dake kan iyaka da Isra'ilar.

Wani Ba- Falasɗine daya shaida lamarin ya ce wuraren da jiragen suka kai harin harda wani wurin binciken da jami'an 'yan Sanda suka kafa, wanda ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas dake kula da lamura a zirin na Gaza, kana da wani sansanin bayar da horo ga reshen mayaƙan ƙungiyar ta Hamas wanda aka fi sani da dakarun Ezzedine al-Qassam. Tuni suma mayaƙan ƙungiyar ta Hamas suka mayar da martani da jefa wasu rokokin a safiyar wannan Talatar, waɗanda kuma suka fa'ɗa a lardin Eshkol na Isra'ila, ko da shike kuma babu rahoton jikkata wani. A makon jiya ne mayaƙan ƙungiyar guda biyu suka mutu sakamakon arangama da sojojin Isra'ila akan iyaka.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadissou