Taron Kolin OIF ya dage zaben sabon shugaba
November 16, 2026
Kungiyar OIF ta kasashe masu magana da harshen Faransanci wadanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka makamnciyar kungiyar Commonwealth ta kasashe renon Ingila mai mambobin kasashe 53 ta so ta zabi sabon sakatare Janar a taron da suka gudanar a Phnom Penh babban birnin kasar Cambodia amma hakan bai yiwu ba.
Bayan da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta fice daga zauren taron, sauran wakilai suka dage zabe zuwa bayan shekara guda inda suka umarci mai rike da mukamin sakataren ta yanzu Mushikiwabo ta Ruwanda ta ci gaba da rike matsayin zuwa wannan lokaci.
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta yi barazanar ficewa daga kungiyar ta OIF idan aka sake zabar Mushikiwabo domin tazarce a karo na uku, inda suka gabatar da nasu dan takarar.
Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango dai na zargin Ruwanda da mara wa kungiyar yan tawayen M23 baya wadda ta kwace yankuna da dama na kasar, zargin kuma da Rwanda ta musanta.