1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci a kasar Kenya

January 9, 2013

Kasar Kenya dai na daya daga cikin kasashen Afrika da ke yawan fuskantar rigingimun kabilanci wanda kuma ke salwantar da rayukan jama'a.

Hoto: Reuters

Wasu rahotani da suka zo muna daga Nairobi babban birnin kasar Kenya,sun yi amanan cewar a kalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hargatsin kabilanci da ya barke a wani kauye da ke kudancin kasar.
Wani babban jami'in hukumar 'yan sanda na nairobi, da a bukaci a saka labule ga sunansa,ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar an samu gawarwakin mutane 8 da aka kone kurmumus,daga ciki har da yara da mata,sannan kuma aka kone wasu gidaje da dama yayin da wasu mutane 9 suka jikata.
kasar dai ta Kenya na yawan fama da riginginmun kabilanci,inda ko a karshen watan Augustan shekarar bara,kimanin mutane 67 suka rasa rayukansu a wani makamancin hakan.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Umaru Aliyu