An hallaka mutane da dama a yankin Darfur
January 2, 2020Talla
Rahotanni sun ce rikicin ya barke a tsakanin 'yan kabilun larabawan yankin inda dauke da bindigogi mutanen suka yi ta harbin juna da kukkona gidajen jama'a lamarin da ya kara kazancewar adadin wadanada suka jikkata.
Hukumomin kasar ta Sudan sun kakaba dokar tabaci a yankin, kana kuma tuni wata tawagar ta musamman ta hukumomin kasar ta isa a birnin El Geneina, inda aka kara karfafa matakan tsaro.