1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci ya barke a kudancin Najeriya

Muhammad Bello
April 20, 2023

Rikicin kabilanci ya barke a birnin Yenagoa na jahar Bayelsa da ke kudancin Najeriya, bayan kisan da wani dan keken haya bahaushe ya yi wa wani fasinja dan asalin jihar.

Hoto: Afolabi Sotunde/Reuters

An samu barkewar sabon rikici a birnin Yenagoa na jahar Bayelsa da ke kudancin Najeriya, sakamakon kisan da aka nunar wani dan keken haya bahaushe ya yi wa wani Fasinja dan jihar ta Bayelsa, inda kuma nan take jama'a su ma suka far wa dan keken suka halaka shi. Yanyin dai yanzu ya haifar da zanga zanga a yau Alhamis, ko da yake rundunar tsaro ta ce ta iya shawo kan matsalar kawo yanzu.

A jiya Laraba ne dai wannan tashin hankali ya soma, yayin da wani mai hayar keken a daidaita sahu a birnin Yenagoa, ya bukaci kudinsa daga wani Fasinja da ya dauka a unguwar Kpansia da ke Birnin.

Kememen da Fasinjan ya yi na ba da cikakken kudi har Naira 100, ya haifar da ka-ce-na-ce tsakanin direban na keken a daidaita din da kuma fasinjan, kuma kafin ka ce me, direban keken ya jawo wata sharbebiyar wuka ya kirba wa fasinjan, inda nan take ya ce ga garinku nan. Su kuma jama'ar tsukin gurin su kuma suka dau hukuncin kashe dan hayar keken nan take.

Hoto: dapd

Yanayin dai ya haifar da tashin hankali, inda jama'a musamman mata suka fito kan tituna a yau Alhamis suna zanga-zangar cewar, da fulani da 'yan ci-rani 'yan arewa da ke jihar su kwashe nasu i nasu, su bar jahar.

Wani Dakta Kakiri Wanigidu Bamu, dan jihar ta Bayelsa ne, ya ce wannan zanag-zanga ina jin za ta ci gaba, domin mutane na da masaniyar cewar kisan gilla irin wannan na ganganci ba shine karon farko ba.

Al Husseni Jibo,da ke zaman tsohon shugaban 'yan arewa a jahar, ya ce al'amarin ta kai da shugabancin alummar ta hausawa da ma bangaren al'ummar unguwar ta Kpansia a birnin na Yenagoa gudanar da taron cimma masalaha da gwamnan jihar.