1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci ya kashe gomman mutane a Chadi

November 1, 2026

Gwamnatin Chadi ta tabbatar da mutuwar akalla mutum 25, yayin da wasu 22 suka jikkata a wani rikicin kabilanci kan amfani da ruwa a yankin tsakiyar kasar.

Weltspiegel 28.04.21 | Demonstration im Tschad | Tableau
Hoto: Issouf Sanogo/AFP

Rikicin ya barke ne a ranar Juma’a bayan sabanin da ya shiga tsakanin wani makiyayi dan kabilar Kreda, wanda ya kai shanunsa shan ruwa a wani tafki, da wani dan kabilar Kuka. Wani dan majalisar yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa makiyayin ya harbi dayan mutumin a kafa, lamarin da ya haddasa musayar wuta tsakanin al’ummomin biyu.

Hukumomi sun ce an shawo kan lamarin kuma tuni aka kama mutum 39 tare da kai su babban birnin kasar, N’Djamena.

Ana yawan samun rikice-rikice kan ruwa da filaye da dabbobi a Chadi, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana cikin kasashen Afirka da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi.