Rikicin kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
February 3, 2013 Fadar gwamnatinJuba,ta zargi dakarun kasar Sudan ta Kudu da kai hare hare a yankunan kasarta inda jiragen yaki suka yi aman wuta a kan wani ayarin motocin sojin Sudan ta Kudu inda daya daga cikin sojojin ya rasa ransa.,yayin da wasu hudu suka jikata.
To saidai kamar kullum a duk lokacin da hakan ta faru,gwamnatin Khartum,ta yi watsi da zargin. Tun lokacin da kasar sudan ta balle daga kasar Sudan ana yawan samun rikici tsakanin kasashen biyu musamman a kan arzikin man fetur da Allah ya huwacewa yankin da ake takaddama a kanshi.
Ko a cikin watan Janairun nan an gudanar da wasu tautaunawa tsakanin magambatan kasashen biyu a birnin Adis Abbaba na kasar Habasha ba tare da an cimma wani daidaito ba.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Halima Balaraba Abbas