Rikicin kan zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP
June 3, 2013Wannan mataki da shugaban kwamitin amintattu na Jamiyyar PDP din Cif Tony Anenih ya sanya kara jan layi da ma kama hanyar raba gari a tsakanin 'ya'yan jamiyyar da tun da dadewa su ke dakon lokacin da za su faffata a zaben fidda gwani na jamiyyar ta PDP da ke fuskantar karin rigingimu a cikinta, wadanda ke dada tasiri ba a jamiyyar ba kadai ba, har ga dimukurdiyyar Najeriyar.
Ganin cewar tuni tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba za ta sabu ba, kuma ma yunkurin da Cif Tony Anenih ke yi na baiwa shugaba Jonathan ikon zama dan takarar jamiyyar ba tare da yin zaben fidda gwai ba ya sabawa tsarin mulkin jamiyyar.
To ko wacce illa ke tattare da wannan ga dimukurdiyyar jamiyyar da ma tsarin dimukurdiyyar Najeriyar, musamman ganin yadda zaben 2015 da sauran kusan shekaru biyu amma ya fara daukan dumi a kasar?
Ra'ayi dai na sha bambam a kan wannan batu da ya tada famin da ke a zukkatan mafi yawan 'yan siyasar Najeriyar da ke jamiyya mai mulki, saboda yadda aka gudanar da zabubbukan fidda gwani na jamiyyar a zabukan baya.
Sanin cewar wannan lamari ne na cikin gidan jamiyyar ta PDP da kalubalen da ta ke fuskanta na rigingimun cikin gida ke kara daukar sabon salo, musamman a game da sakamakon zaben kungiyar gwamnonin kasar da ba kawai ta kara raraba kawunan gwamnonin jamiyyar ba, ake ma hasashen yi wa wadanda ke ja da dan takarar da gwamnatin ta tsayar bita da kulli, abinda ya sanya kara nuna damuwa a kan inda aka dosa.
Da alamun dai kwarewar da a kan yiwa shugaban kwamitin amintatu na jamiyyar ta PDP na gyara rikita-rikitar siyasar jamiyyar PDP a wannan karon ya furta mai zafi da maimakon gyara na iya watsa kawunan yayyan jamiyyar yama yi tasiri ga dimukuirdiyyar Najeriyar.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu