1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RIKICIN KARE DARAJAR EURO, TSAKANIN HUKUMAR TURAI DA TARAYYAR JAMUS.

Yahaya Ahmed.November 19, 2003
Babban jami'in kula da harkokin kudi na Hukumar Tarayyar Turai, Pedro Solbes, bai bata lokaci ba wajen shawo kan takwarorinsa ga amincewa da matakan da za a dauka kan gwamnatin Jamus, saboda saba wa ka'idojin hukumar da ta yi, na zarce gibin kasafin kudinta da kashi 3 cikin dari. Kafin dai a fara amfani da kudin nan na Euro, duk kasashen da ke cikin shacin kudin, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya, wadda ta tanadi kare darajar Euron. Daya daga cikin matakan ganin cewa darajar kudin ta kasance daram kuwa, shi ne kayyade wa ko wace kasa, haddin da bai kamata ta tsallake ba, a gibin da za ta samu na kasafin kudinta a ko wace shekara. A halin yanzu dai, basussukan da Jamus ke da su, sun zarce kashi 3 cikin dari na kudaden shigarta. Wannan kuma, shi ne karo na 3 a jere da kasar ta sami kanta cikin wannan halin. Sabili da haka ne dai, Hukumar Taryyar Turan, mai sa ido kan ganin cewa, an kiyaye ka'idojin kare darajr Euron, ba ta yi wata wata ba, wajen lakaba wa Jamus wasu sharuddan da za su kayyade yadda za ta tsara kasafin kudinta a cikin shekaru 2 masu zuwa.

A zahiri dai, abin da wannan matakin ya kunsa, shi ne tilasa wa ministan kudin Jamus Hans Eichel, rage gibin kasafin kudin da Jamus ke samu, sakamakon komadar tattalin arzikin da take huskanta, da kashi sifili da digo 8 cikin dari a cikin wannan shekarar. Manazarta harkokin tattalin arziki dai na ganin cewa, Hukmar ta nuna sassauci ga Jamus. Saboda, da za ta bi dokokin ne kamar yadda aka tsara su, da an ci Jamus din ma tarar kudi na miliyoyin Euro. Amma babban jami'i Solbes ya karfafa cewa, a shekara ta 2005, Hukumar za ta tsananta zartar da dokokin, idan Jamus ta sake zarce haddin gibin kashi 3 cikin dari na kasafin kudinta. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

"Hukumar za ta yi wa Jamus afuwa ne ta shekara daya, don ba ta damar yi wa gibin kasafin kudinta gyara, kamar dai yadda aka yi wa Faransa. Kafin kuwa ta iya dawowa a gibi na kashi 3 cikin dari a shekara ta 2005, kamata ya yi tun yanzu ta dau matakan karfafa kasafinta na shekara mai zuwa."

Wannan shawarar da hukumar ta yanke a kan Berlin dai, kwatankwacin wanda ta yanke wa Paris ne a wasu `yan makwannin da suka wuce. Bisa dukkan alamu, a shekarar badi, ita ma Faransan za ta zarce haddin kashi 3 cikin dari na gibin kasafin kudinta, a cikin shekaru 3 a jere. Sabili da hakan ne dai, Pedro Salbes ya yi barazanar tsananta zartar da dokokin ma a kan Faransa, a shekara mai zuwa. A ran litinin da talata mai zuwa ne, ministocin kudi na kungiyar Hadin Kan Turai za su yi taronsu a birnin Brussels don tattauna wannan batun. Game da hakan ne dai Solbes ya bayyana cewa:-

"Ina fata za a yi kyakyawar muhawara a mako mai zuwa. Ina kuma kyautata zaton cewa, za a gabatad da duk alkaluman da suka shafi wannan batun a zahiri."

Amma kafin Hukumar ta iya daukan wani sahihin mataki, sai ministocin kudin, sun amince da shawarwarin da za ta gabatar, da rijayin kashi biyu bisa uku. Hakan kuwa zai yi wuyar samu, saboda babu shakka, ministocin Faransa da Jamus za su yi watsi da shawarar, kamar dai yadda suka yi a makwannin biyun da suka wuce, inda suka hana tsai da shawarar daukan mataki kan Faransa. Italiya ma za ta bi sahun Faransan da Jamus, saboda ita ma tana da matsalolin kasafin kudi.

Ministan kudin Jamus Hans Eichel dai, ya bayyana cewa, shawarar hukumar ba ta da wani muhimmanci gare shi. A nasa ganin, Jamus na ba da cikakken hadin kai ga hukumar, kuma tana daukan tsauraran matakan tsimi don inganta halin kasafin kudinta. Sabili da haka ne ya ga bai kamata a wuce gona da iri da tsuke latlita ba, musamman ma dai a lokacin komadar tattalin arziki. In ko ba haka ba, duk wasu sabbin matakai masu tsananin da za a dauka, ba za su magance kome ba, sai dai ma su tsawaita lokacin da Jamus za ta sami kanta cikin matsin tattalin arziki, inji Hans Eichel.