1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin kwace jiragen shugaban Najeriya

August 16, 2024

Najeriya ta ce tana shirin bin hanyoyin dawo da jiragen shugaban kasar guda Uku da wata kotu a Faransa ta bai wa wani kamfanin China, yan Najeriyar na nuna damuwa kan matakin da ke neman bata sunan kasar a idanun duniya

Hoto: picture-alliance/dpa/R. Schlesinger

Takkadama dai tai nisa a tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriyar da kamfanin Zhongshan Fucheng na kasar Sin bisa wasu jiragen sama guda Uku na shugaban kasar da kamfanin yai nasarar karbewa.

Wata Kotu da ke birnin Paris ce dai ta bai wa kamfanin damar karbe jiragen sakamakon wani rikicin da ke tsakaninsa da daya daga cikin jihohin Najeriya guda Uku.

A shekarar 2007 ne dai kamfanin ya rattaba hannu don kafa cibiyar ciniki maras shinge da Jihar Ogun, kafin rikicin ya kai su ga kotun wadda ta amince jihar ta biya kamfanin tsabar kudi dala miliyan 60.

Duk da cewar Abujar ta ce tana shirin yin dukkan mai yiwuwa da nufin sake dawo da jiragen , tuni nasarar kamfanin na kame jiragen da ke a birnin Paris ya tada hankalin yan kasar dama.

Dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi dai ya ce matakin yana zaman abun kunya a bangaren masu mulkin kasar.

Da kyar da gumin goshi ne dai alal ga misali Abujar ta yi nasarar kauce wa aman wasu tsabar kudi dala miliyan dubu 11 da wani kamfanin kasar Ingila ke nema bisa wata kwangilar iskar gas  a kasar.