1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kwango da kokarin Jamus na samun makamashi a Afirka

Usman Shehu Usman ZMA
December 9, 2022

Kungiyar M23 na ci gaba da haddasa asarar rayuka a cewar Jamhuriyar Demokradiyya Kwango da kokarin Jamus na neman makamashi daga kasashen Afirka.

'Yan Kwango da ke adawa da mayakan M23
'Yan Kwango da ke adawa da mayakan M23Hoto: Aubin Mukoni/AFP

A wannan makon zamu fara ne da jaridar die Tageszeitung, wace ta yi sharhi kan tashin hankali da ke faruwa Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango. Inda jaridar ta ce gawarwaki na karuwa kuma babu tabbas su waye ke aiktawa.

Ita dai gwamnatin Kwango na zargin 'yan tawayen M23 da kisan gilla, kuma tana bayar da rahoton mutuwar mutane da dama. Amma me ya gaskiyar abin da ya faru a Kisheshe? Kauyen na kan gaba ne na mayakan Hutun kasar Rwanda FDLR. Mai yiwuwa shi ne kisan gilla mafi girma a cikin 'yan shekarun nan a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.

Gwamnati ta sanar da mutuwar mutane 272  a yammacin Litinin da ya gabata a karamin garin Kisheshe da ke gabashin kasar tare da dora alhakinsu kan mayakan M23. Hukumomin shari'a na Kwango da kuma sashen kare hakkin bil'adama na tawagar MDD Monusco na gudanar da bincike kan kisan.

Ministan tattalin Jamus Robert Habeck a Afirka ta KuduHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Sai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wace ita kuwa ta duba laluben Jamus na samun makamashi daga Afirka. Jaridar ta ce Ministan tattalin arziki Robert Habeck na ziyarar neman abokan hulda a Afirka.

Kasashen dai na da muhimmacin a matsayin abokan huldar samar da makamashi da kawar da gurbataccen mai, in ji ministan tattalin arzikin Jamus Robert Habeck a ranar Laraba a taron kolin tattalin arzikin Jamus da Afirka a kasar Afirka ta Kudu. Don yin wannan, duk da haka, dole ne a fara fadada makamashin da za a iya sabuntawa a cikin kasashen Afirka, wanda shi ne babban makasudin shirya taron.

Shirin samar da makamashi mai tsabtaHoto: imago images

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung  ta yi labarin na kasar Jamus da Afirka, amma kuma ta maida hankali ne kan bukatar makamashi daga kasar Namibiya. Inda jaridar ta dora da cewa Jamus na bukatar makashi cikin gaggawa don sanya tattalinta kan turbar da ta dace, yayin da a gefe guda ita kuwa Namibiya na da wadatar filaye, kuma rana da iska su na lalacewa ba a cin muriyarsu.

Don haka jaridar ta ce da alama hadin gwiwar na iya zama wani abu mai alheri ga dukkan kasashen biyu. Manyan Kamfanonin mai, su ma sun fara aiki sannu a hankali. Inda tuni wasu kamfanonin Jamus suka rungumi kasada tare da tsunduma a harkokin kasuwanci na samar da makashi marar gurbata muhalli.