1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Libiya yana ƙara ta'azzara

March 22, 2011

Ana ci gaba da yin tababa game da makomar hare haren da sojojin ƙasashen yammacin duniya ke kaiwa akan Libiya, a yayin da jiragen yaƙin suka shiga dare na uku a jere suna luguden wuta akan birnin Tripoli.

Gidan Gadhafi a Tripoli, bayan harin da sojin yammaci suka kaiHoto: AP

A yayin da dakarun ƙawance ke bayyana gamsuwa game da irin ci gaban da suka samu ya zuwa yanzu wajen rage ƙarfin naurorin bada kariya ga sararin samaniyar ƙasar Libiya, wani babban jami'in sojin Amirka ya bayyana yiwuwar rage hare haren jiragen saman da ƙasashen yammacin duniyar suka ƙaddamar amma ya ce akwai buƙatar faɗaɗa yankunan da ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya ya tanadi haramtsa yin shawagin jiragen saman ya zuwa sauran sassan ƙasar baki ɗaya. A cewar Janar Carter Ham, babban hafsan dakarun Amirka a yankin Afirka, faɗaɗa hurumin za ta basu damar samun babban 'yancin yin walwala.

Ƙasar Amirka dai ta ce ba ta da wata anniyar ci gaba da jagorantar hare haren jiragen yaƙi a ƙasar Libiya, wanda kuma firaministan Birtaniya David Cameron ya ce akwai aniyar miƙa ragamar yaƙin zuwa ga ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO, amma Faransa ta ce ƙasashen Larabawa ba sa ƙaunar ganin Amirka dake jagorantar ƙawancen ne za ta ´zama ja-gaba wajen yaƙi a ƙasar ta Libiya, wadda ke da arziƙin man fetur. A cewar David Cameron duk ƙoƙarin da suke yi shi ne kare fararen hula:

" Wannan yana da banbanci da ƙasar Iraƙi. Wannan ba wai shiga cikin wata ƙasa da nufin tumɓuke gwamnatin ta da kuma ɗaukar alhakin dukkan abinda ya biyo bayan hakane ba. Wannan batu ne daya danganci kare Libiyawa da kuma basu damar tsara makomar su."

Shugaba Obama yana yin tsokaci akan rikicin LibiyaHoto: AP

Yunƙurin kawar da Gaddhafi daga mulki

Magoya bayan shugaba Gaddhafi dai suka ce idan har da gaske ne ƙasashen yammacin duniya ke yi na kare buƙatun fararen hula, to menene dalilin ƙaddammar da hare haren bama bamai akan filayen jiragen sama da kuma wasu tashoshin jiragen ruwa, game da fadar shugaban ƙasa - tunda a cewar kakakin gwamnatin Gaddhafi babu makkamai a wuraren. Sai dai kuma a tsokacin daya yi ga matsayin Amirka, shugaba Obama na ƙasar cewa ya yi ƙoƙarin aiwatar da manufar ƙasar sa yake akan Libiya:

"Na bayyana a fili cewar Manufar da Amirka ta sanya a gaba ita ce kawar da Gaddhafi, kuma muna da hanyoyi daban daban na cimma wannan burin baya ga matakin sojin da muke ɗauka wajen tallafawa manufar."

Harin dakarun gwamnati akan 'yan tawaye

A faɗan da aka yi a baya - bayan nan kuwa tashar telebijin ta Al-Jazeerah wadda ke da cibiya a Qatar, wato ƙasar Larabawar dake sahun farko wajen ƙawancen kaiwa Libiya hari, ta ruwaito cewar dakarun dake goyon bayan Gaddhafi sun yi ta buɗe wuta akan mazauna garin Zintan ta hanyar amfani da manyan tankokin yaƙi. Hakanan a can Misurata ma wani mazaunin birnin ya koka game da halin dakarun gwamnatin:

"Abinda yake sabo a birnin Misurata shi ne cewar dakarun dake goyon bayan shugaba Gadhafi suna tilastawa ɗaukacin mazauna birnin dama na garuruwan dake kewaye da ita barin matsugunan su. Suna tilastawa mata da ƙananan yara riƙe tutocin dake da launin kore, kana da umartarsu da yin jerin gwano a babban titin dake ƙarkashin ikon shi Gaddhafin.

A halin da ake ciki kuma a wannan Talatar ce jami'an ƙungiyar ƙawancen tsaton NATO ke komawa taro a birnin Brussels, bayan da suka gaza cimma matsaya guda akan batun rikicin na Libiya a jiya Litinin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadissou

***