Rikicin Libya na bukatar tallafin kasa da kasa
February 17, 2015Shugaba Abdel-Fattah al-Sissi na kasar ta Masar a ranar Talatan nan ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya shiga tsakani kan rikicin da ke faruwa a kasar Libya, kwanaki biyu bayan da mayakan IS suka fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda suka yanka wasu mabiya addinin Kirista 'yan asalin kasar ta Masar guda 21.
A cewar shugaba al-Sisi akwai bukatar samun goyon baya wajen shigar al'ummar kasar ta Masar da ma gwamnatin kasar kan duk wani yunkuri na shiga tsakanin.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a zantawarsa da gidan rediyon Europe 1 na kasar Faransa bayan da dakarun sojan sama na kasar ta Masar suka yi lugudan wuta a kan mayakan na IS kwana guda da ya gabata.
Shi kuwa jakadan Majalisar Dinkin Duniya Bernardino Leon da ke sanya idanu kan ayyukan hukumar a kasar ta Libya, ya bayyana cewa akwai tanade-tanade da ake da su a kasa muddin shirin samar da sulhu a tsakanin bangarori masu adawa da juna ya gaza nasara.