Rikicin makaman nuklear Iran
June 1, 2007Kasar Iran, ta bayyana aniyar komawa tebrin shawarwari tare da hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta MDD.
Ta bayyana hakan, a sakamakon ganawar da aka yi jiya, tsakanin sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai Havier Solana, da kuma shugaban tawagar Iran a tanttanawar rikicin nuklea Ali Larijani.
Solananya bayyana gamsuwa, a game da ci gaban da aka samu a wannan badaƙala.
Idan dai ba a manta ba, ƙasar Iran ta yi tsayuwar gwamen jaki, a game da buƙatocin Majalisar Ɗinkin Dunia na ta yi watsi da aniyar mallakar makaman nuklea.
Tawagogin 2, sun yanke shawara sake gamuwa, nan da makwani 2 masu zuwa, domin ci gabada tantanawa.
Saidai a yayin da ta ke maida martani, sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice, ta ce, ci gaban da a ka ce an samu a taron na jiya, irin na mai haƙar rijiya ne.