Rikicin makaman nuklear Iran
February 21, 2007Talla
Tawagogin Iran da na ƙungiyar hanna yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia, sun gana jiya a birnin Vienna.
Shugaban tawagar Iran Ali Larjani, da shugaban hukumar IAEA Mohamed Albaradei,sun cenza miyau, a kan hanyoyin cimma nasarar warware rikici makaman nuklear ƙasar Iran.
Jim kaɗan kamin wannan ganawa, shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahamadinejad, ya sake jaddada matsayin sa, na ci gaba da aiki, amma ya alkawarta cin tuwan fashi, da sharaɗin ƙasashen turai da Amurika, suma, su dakatar da nasu shiri, ta wannan fanni.
Sannan Ahmadunedjad, ya bayyana yiwuwar warware taƙƙadamar ta hanyar diplomatia, saidai ya yi wasti da sharrudan da Amurika ta gindaya, na cewar sai Iran ta dakatar da shirin kamin fara tantanawar.