1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin makiyaya da manoma ya hallaka mutane 16 a Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 25, 2023

Rundunar sojin Najeriya ta ce rikicin ya barke ne da tsakar daren Asabar, a Kauyen Mushu da ke tsakanin kananan hukumomin Mangu Bokkos

Hoto: AP

Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 a jihar Filato da ke tarayyar Najeriya, kamar yadda rundunar sojin kasar ta tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Karin bayani:Rashin tsaro na mummunan tasiri kan noma a jihar Filato

Mai magana da yawun dakarun Safe Haven da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihohin Filato Bauchi da kuma Kaduna Kyaftin Oya James, ya shaidawa AFP cewa rikicin ya barke ne da tsakar daren Asabar, a Kauyen Mushu da ke tsakanin kananan hukumomin Mangu Bokkos.

Karin bayani:Martani mabanbanta kan sakin Joshua Dariye

Ya kara a cewa tuni suka baza jami'ansu domin dakile duk wani yunkuri na sake tayar da hankali a yankin. Kasancewar jihar ta yi kaurin suna wajen fuskantar rikice-rikice irin wannan.