1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin makiyaya da manoma ya hallaka mutane 21 a Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 5, 2024

Mr Mark ya ce makiyayan sun yi ramuwar gayya ne a daren Alhamis, bayan kashe musu mutane 6 kwanaki 3 da suka gabata, kuma a Juma'ar nan aka yi jana'izar mutane 21 din da suka mutu

Hoto: Jossy Ola/AP Photo/picture alliance

Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 21 a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda shugaban karamar hukumar Omala Mr Edibo Ameh Mark ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Karin bayani:Rikicin makiyaya da manoma ya hallaka mutane 16 a jihar Filato da ke Najeriya

Mr Mark ya ce makiyayan sun yi ramuwar gayya ne a daren Alhamis, bayan kashe musu mutane 6 kwanaki 3 da suka gabata, kuma a Juma'ar nan aka yi jana'izar mutane 21 din da suka mutu.

Karin bayani:Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya

Rikicin makiyaya da manoma dai ba sabon abu bane a Najeriya musamman a yankin arewaci, wanda ya jima yana janyo asarar rayukan mutane da dabbobi.