1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Siyasar Mali da Zambiya sun dauki hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman MA
August 20, 2021

A wannan mako jaridun Jamus sun dubi nasarar Hakainde Hechilema a Zambiya da batun bai wa 'yan Afghanistan mafaka a Yuganda.

Sambia Luska | Oppositionskandidat | Hakainde Hichilema
Zabebben shugaban kasar Zambiya, Hakainde HechilemaHoto: Salim Dawood/AFP/Getty Images

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus daga kasar Mali, inda jaridar die tageszeitung wanda ta ce an yi babban bikin cika shekara guda da sojoji suka kifar da gwamnati a Mali.

A ranar 18 ga watan Agustan 2020, sojoji suka sauke gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita a Mali, inda suka kawo karshen gwamnati da cin hanci ya mamaye, wanda kuma shugaba mai bakin jini ke jagoranta. Cikin gaggawa sojoji suka sanar da gwamnatin da zai jagoranci kasar i zuwa zabe, amma kuma kafin a cika shekara daya sai aka sake wani juyin muki wanda ya tabbatar mika komai a hannun sojoji. Sojojin dai sun yi alkawarin gudanar da zabe a farkon badi.

Hoto: Francis Kokoroko/File Photo/Reuters

A lamarin da ya shafi kasar Mali. Jaridar Der Tagesspiegel wanda ta ce yadda Taliban suka karbe iko da kasar Afghanistan cikin sauri hakan ya aza yar tambaya a kan amfanin sojojin Jamus a kasashen waje. Jaridar ta ruwaito ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer tana mai cewa Ya kamata mu koyi darasi kan aikin wanzar da zaman lafiya da dakarun Jamus ke yi.

Ministar ta kara da cewa muna bukatar tantance sauran sojojinmu da ke aiki a kasashen waje, mu duba cewa shin zaman namu ya yi, me yakamata mu kara gyarawa?

die tageszeitung ta dora kan batun Agfanistan. Inda ta ce kasar Amirka ta cimma yarjejeniya da kasar Yuganda don kwaso ‘yan Afganistan 2000 zuwa Yuganda. Tuni ma dai shugaban majalisar dokoki ya sanar wa takwarorinsa cewa, kimanin 'yan gudun hijira daga Afganistan 2000 ake dakon isowar su a Yuganda. Tuni ma dai Firaministan kasar ya rubuta wa ma'aikatar lafiya wasika, don neman su shirya yin gwajin COVID-19 wa 'yan Afganistan da za a kwason.

Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

Minista mai kula da 'yan gudun hijira tuni ya fada wa manema labarai cewa a ranar Larabar da ta gabata jirgin yakin Amirka ya kwaso 'yan Afganistan 500. Ita kuwa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta sanar da shirya otel da za a sauki bakin daga Afganistan.

 

Sai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wacce ta ce yanzu akwai fatan habakar tattalin arziki a Zambiya. Ta ce dalili kuwa shi ne madugun 'yan adawa Hechilema da ya lashe zabe. Jaridar ta ruwaito wani mai gabatar shirye-shiyen radio a Lusaka, wanda tun sanyin safiya ya fito ya yi ihun cewa Allah ya karbi addu'arsu, inda jaridar ta ci gaba da cewa madugun adawa Hakainde Hichilema ya kafa tarihi bayan da hukumar zabe ta ayyana cewa ya samu kuri'u miliyan biyu da dubu 800, yayin da shi kuwa shugaba mai ci Edgar Lungu, ya samu kuri'u miliyan daya da dubu 800.