1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Masar ya ɗau sabon salo

Usman ShehuJuly 25, 2013

Sojoji a ƙasar Masar na ƙara nuna alamun murgushe duk wanda yaƙi miƙa wuya bisa umarninsu

epa03769756 (FILE) A file photo dated 22 May 2013 shows Egyptian Minister of Defense Abdel-Fattah al-Sissi while receiving seven Egyptian security personnel, who were released by unknown kidnappers in the Sinai Peninsula, at Al-Maza military airport in Cairo, Egypt. The army on 01 July gave Egypt's political factions a 48-hour ultimatum to reach consensus and meet the people's demands or it would announce a series of measures to end the stalemate. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Abdel-Fattah al-Sissi, babban hafsan sojin MasarHoto: picture-alliance/dpa

Sojoji a ƙasar Masar sun baiwa ƙungiyar Muslim Brotherhood kwanaki biyu da su shiga shirin gwamnati ko kuma su gamu da fushin hukuma. Wani kakakin sojojin ƙasar yace basu da niyyar cin zarafin wani, amma kuma ba za su lamunta da ci gaba da boren adawa da gwamnati da kuma ta'addanci ba. Dama dai tun a jiya shugaban askarawan sojan Masar ya nemi da a fito kan titi a gobe domin baiwa sojoji hallarcin murgushe duk mai adawa da su hukuma wanda ke neman tada ƙayar baya. Ƙasashen duniya dai na ci gaba da fargaban cin zarafin ɗan Adam, bisa wannan kiran da babban hafsan ya yi na a fito zanga-zanga, abinda ke nuna alamun hukuma na son yin amfani da karfi kan masu yi mata taurin kai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita:        Umaru Aliyu