Rikicin Nuclear na Koriya ta Arewa
March 19, 2007Talla
Amurka da koriya ta arewa sun cimma warware matsalar dake tsakaninsu adangane da kimanin kudi dalan Amurkan million 25,mallakan Koriyan .Jamian Amurkan sunyi nuni dacewa hakan na bangaren cigab da akasamu dangane da dakatar da shrin nuclearn Koriya ta arewan.Adangane da hakane jakadan Amurka Christopher Hill yace tace tattaunawar kasashe shida da aka koma yau litinin,zai mayar da hankali kann wasu matsaloli,wadanda keda da yawa.Mataimakin sakataren kula da harkokin kudi na Amurka Daniel glaser ya bayyana cewa,bisa ga wannan yarjejeniyar zaa tura wadannan kudade zuwa bankin kasar Sin dake Beijing din,domin inganta harkokin ilimi da rayuwar biladama a koriya ta arewa.