Rikicin nukiliyar kasar Koriya Ta Arewa
October 14, 2006Talla
Kasashe 5 masu ikon hawa kujerun naki a kwamitin sulhun MDD da Japan sun cimma daidato game da matakan jan kunnen da za´a iya dauka kan KTA. Bayan wasu shawarwari masu tsauri da ya yi yau da takwarorinsa na Rasha da Sin, jakadan Amirka a MDD John Bolton ya nunar da cewa ya samu karfin guiwa cewa kwamitin sulhu ka iya kada kuri´ar amincewa da kudurin jan kunnen KTA. A gun taron kasashe 15 membobin kwamitin za´a sake yiwa daftarin kudurin kwaskwarima.
“Yanzu nan muka kammala wani taro na kasashe 5 masu zaunannun kujeru da Japan, kuma zamu ci-gaba da tataunawar da sauran membobin kwamitin sulhu,inda na ke da niyar gabatar dac wasu canje canje masu muhimmanci. Kasancewar mu a nan yana da muhammanci ga kwamitin sulhu ya mayar da martani yau kwanaki 6 bayan gwajin makamin nukiliyar da KTA ta yi.”