Rikicin Pakistan
November 8, 2007Tshohuwar premiyan kasar Pakistan Benezir Bhuto ,tayi kira ga al’ummomin Pakistan dasu gudanar da zanga zangar na bayyana adawa da dokar ta bacida shugaba Pervez Musharraf ya sanya a wannan kasa.Wannan kira na Bhuto yazo ne ,bayanda da jam’iyyar shugaba Musharraf tace ,mai yiwuwa ne shugaban mulkin sojin ya dage dokar ta bacin cikin makonni biyu zuwa uku nan gaba.Bayan ganawarta da shugabannin jam’iyyun adawn kasar,Bhuto ta fadawa manema labaru a birnin Islamabad cewar,wannan mataki da shugaban kasar ya dauka ya sabawa dokar kasa.A baya dai tsohuwar premyan Pakistan din mai shekaru 54 da haihuwa,taki cewa komaia bisa ga zanga zanagar da aka gudanar na tsawon kwanaki uku,na adawa da wannan doka,ammam a yanzu ta sha alwashin gudanar da wannan Gangami a garin Rawalpindi ,a ranar juma’a,duk kuwa da gargadin da jamian yansanda sukayi na yin kame.