1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin PDP a Najeriya na kara ta'azzara

June 6, 2013

Jam'iyyar PDP da ke mulki a Najeriya na ci gaba da dauki dai-dai da wasu daga cikin 'ya'yanta sakamakon rikicin ikon da ta tsunduma ciki.

Auf dem Bild: Parteizentrale PDP (Partei an der Macht in Nigeria) in Abuja, Nigeria. Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Hoto: DW/U.Haussa

A wani abun dake zaman alamu na kara rincabewar rikici, gwamna na biyu cikin tsawon mako biyu yanzu haka na hutun dole a jamiyyar PDP mai mulkin da tai nisa a rijiyar rikicin ikon mulkin kasar na shekara ta 2015.

Rani dai yana kara rani sannan kuma kowa yana shirin gane hanyar garinsu cikin jam'iyyar PDP mai mulkin tarrayar Najeriya. Jam'iyyar kuma da ta dakatar da gwamnonin ta har biyu cikin tsawon kasa da makonni biyun da suka gabata.

An dai karya kummallo ne da Rotimi Chibuke Ameachi dake zaman gwamnan jihar Rivers da kuma ya ja da fadar gwamantin kasar yai nasarar sake darewa bisa shugabancin kungiyar gwamnonin kasar mai tasiri, kafin daga baya jam'iyyar ta nufo arewa inda ta samu gwamna Aliyu Magatakarda na jihar Sokoto da tace ta tura ya zuwa hutun dolen sannan kuma ta zarga da rashin biyyaya a gareta.

Duk da cewar dai a duk karatun gwamnonin biyu dai bakin PDP na ambato kin bin umarnin magabata, a cikin zuciyar ta dai akwai alamu na gani a kokon shan duk wani mai ja da hukuncin fadar gwmantin kasar ta Aso Rock da tai nisa a bukatar tabbatar da sake ci gaba cikin mulkin kasar nan da shekaru biyu.

Alhaji Bamanga Tukur, shugaban jam'iyyar PDP.Hoto: DW/U.Haussa

Ana ma dai kallon dakatar da Wammakon a matsayin babban sako ga masu daure masa gindi a arewacin kasar da suke tunanin suna iya rawar a gaban hantsin jam'iyyar ba tare da amincewar masu juya akalar PDP na Abuja ba.

Tuni dai dama na hannun dama ga shugaba Jonathan suka fara karanta yiwuwar tikitin zarcewa ga shugaban da ma gwamnonin da su ka yiwa PDP biyayya ba tare da gudanar da taruka fidda da gwani ba tarukan kuma da ke iya ban mamaki ga shugaban da sannu a hankali farin jininsa ke raguwa a ciki dama wajen jam'iyyar

Mallam Faruk B. B. Faruk dai na zaman tsohon dan kwamitin kolin jam'iyyar na kasa da yanzu haka kuma ke sharhi kan lamuran PDP, kuma a fadarsa sabon salon dakatarwar dai na zaman wayon a ci ne aka kori kare daga gindin dinya.

Share fage ga shugaba Jonathan ko kuma kokari na tabbatar da da'a a cikin PDP dai, ko bayan dora kowa bisa hanyar da ta dace ya tsaya daga dukkan alamu kuma sabon sakon na iya shafar jam'iyyar da magoya bayanta ke kara rungumar sababbin masu adawar kasar ta Najeriya a kokari na sauyin alkiblar mulkin da ake shirin gani cikin wasu shekaru biyu masu zuwa.

Shugaba Jonathan na Najeriya.Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Gwamnoni biyar kacal cikin 19 na arewacin kasar ne dai suka kai ga halartar taron gwamnonin arewacin kasar da aka kammala da yammaciyar wannan Alhamis (06.0613) a garin Kaduna a wani abin da ke zaman alamu na kara dawowa daga rakiyar tafiyar lamuran PDP.

Akalla gwamnonin PDP kusan takwas da manya da kananan 'ya'yanta ne dai yanzu haka ke kafa guda a ciki daya kuma a wajenta a kan hanyar zuwa ga sabuwar jamiyyar APC da ta tattaro 'yan adawar kasar ta Najeriya wuri guda.

To sai dai kuma a fadar Bala Ka'oje dake zaman babban ma'ajin PDP na kasa babu tada hankalin cikin sabon salon da jam'iyyar ke dauka yanzu haka.

Abin jira a gani dai na zaman yanda za ta kaya a masu tunanin sai ta zarce da kuma masu ganin ta zo karshe ga shugaban kasar da hankalinsa ke rabe tsakanin mulkin kasar da biyan bukatu na kashin kansa.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh