1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta gaza bayyana shirin komawa tafarkin dimukaradiyya

Suleiman Babayo ATB
March 4, 2022

Muhawarar da aka tafka a Majalisar Dinkin Duniya inda kuri'ar da galibin kasashen Afirka suka yi tir da kutsen Rasha a Ukraine na cikin batutuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus.

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da aka soki matakin kutsen Rasha a kan Ukraine
Babban zauren Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Timothy A. Clary/AFP

Jaridar Die Welt ta ce abin mamaki kasashen Afirka sun bijira wa Rasha a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, yayin da China ta duba mihimamncin Shugaba Vladimir Putin na Rasha wajen rashin kada kuri'ar bisa abin da ke faruwa a Ukraine. Kasashen na Afirka ba barazana da suke fuskanta daga kungiyar tsaron NATO, amma Afirka ta fahimmaci wannan magana ce da ta shafi 'yancin kasashe na duniya.

'Yan Afirka da Asiya da suka tsere daga UkraineHoto: WOJTEK RADWANSKI/AFP/Getty Images

Lokacin da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya amince da matakin 'yan awaren gabashin Ukraine na ballewa daga kasar ta Ukraine. Jakadan Kenya a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fito fili ya ce Kenya kamar sauran kasashen Afirka, Turawan mulkin mallaka suka shata iyakokin kasashen kuma duk kan iyakokin an raba mutanen da suke da addini daya da kabila daya gida biyu, amma maimakon neman koma da baya kan tahiri kasashen Afirka sun rungumi yanayin da suka samu kansu tare da aiki tare tsakanin kasashen wanda shi ne abin da ya dace a yi tsakanin Rasha da UIraine maimakon kutse mamaya da yaki.

Sai jaridar Süddeutsche Zeitung da ke cewa kasashen Rasha da Ukraine suna da tasiri wajen fitar da kayayyakin amfanin gona, kuma wannan kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine zai shafi kasashe masu tasowa na duniya da suka dogara kan kasashen biyu. Jaridar ta kara da cewa wannan yaki zai shafi farashin kayan amfanin gona da kasashen biyu ke fitarwa zuwa galibin kasashe na Afirka da Asiya, kuma halin da ake ciki zai iya kara yunwa a kasashe masu tasowa. A shekarar da ta gabata ta 2021 kasar Ukraine ya fitar da kayayyakin amfanin kimanin ton milyan 33 galibi zuwa kasashe masu tasowa.

Hoto: Ebrahim Hamid/AFP/Getty Images

Jaridar Tageszeitung ta yi sharhin mai taken kasar Sudan tana tsaka mai wuya. Wani jami'in diflomasiyya na Jamus ya bayyana irin hassala da ake da ita game da yadda wakilan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya suka gaza nuna shirin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya, ga kuma yadda sojojin ke ci gaba da amfani da karfi kan masu zanga-zanga.

Ana ta bangaren jaridar Neues Deutschland ta ce duk da matakin Jamus kan shirin yarjejeniyar kan Jamus za ta biya kasar Namibiya wasu kudade kan abin da ya faru na tarihi kan kisan kare dangin al'ummomin Herero da Nama yayin mulkin mallaka a farkon karnin da ya gabata. Jaridar ta ce har yanzu akwai masu tunanin Jamus tana neman kauce wa nauyin da ke kanta na tarihi. Jamus tana cikin kasashe da fuskantar suka kamar Birtaniya da Faransa, da Potugal da Spain na abubuwan da suka faru a kasashen masu tasowa lokacin mulkin mallaka.