Rikicin sakamakon zaɓe ya kashe mutane 300 a Kenya
January 2, 2008Shugaba Mwai Kibaki na ƙasar Kenya ya zargi shugaban jamiiyyar Adawa kuma abokin takararsa a zaɓen shugaban kasa daya gabata Raila Odinga,da haifar da kisan kiyashi .Wadannan kalamai na shugaban kasar sunzo ne adaidai lokacin da yawan wadanda suka rasa rayukansu a fadan bayan zaɓen ya kai 300.Sanarwar data fito daga gwamnatin Kenya ta bakin ministan kula da harkokin kasa Kivutha Kibwana,na dora alhakin tashe tashen hankulan da kasar ke fama dasu akan jamiiyyar adawan ta Odinga.Sai dai ministan harkokin wajen Britania David Miliband ya jaddada cewar hakki ya rataya a wuyan bangarorin biyu na kawo karshen wannan asaran rayuka dacewar“muna sane dacewar hakki ya rataye a wuyan dukkannin bangarorin biyu na tabbatar da tsarin siyasa.Yana da muhimmanci a tuna cewar akwai zaɓuɓɓuka a wasu ƙasashen Afrika cikin watanni 18 masu gabatowa da suka haɗar da Angola da Ghana da Malawi,domin Kenya tana da matukar tasiri acikin su da ita kanta“