1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin Senegal: Sall zai bar mulki a watan Afrilu

February 23, 2024

Bayan matsin lamba a ciki da wajen Senegal, shugaba Macky Sall ya sanar da sauka daga mulki kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulkin kasar duk da cewa bai sanar da ranar da za a gudanar da da zabe ba.

Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall Hoto: John Thys/AFP

Sall ya sanar da hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai ta kafar talabijin, inda ya jaddada cewar zai bar mulki a ranar 2 ga watan Afrilu duk da kalaman na sa na da sarkakiya kasancewar ba a san wanda za a damka wa kasar ba, kuma bai sanar da ranar da za a gudanar da zabe ba.

Kotun Kundin Tsarin Mulkin Senegal ce ta umarci Sall da ya sanya ranar da za a gudanar da zabe nan ba da dadewa ba, duk da cewa har yanzu bai aiwatar da umarnin kotun ba.

Senegal ta shiga rudanin siyasa tun bayan da shugaba Macky Sall ya sanar da daga babban zaben kasar zuwa watan Disamba sakamakon zargin cin hanci da rashawa a ayyukan hukumar zaben kasar da kuma dambarwar tantance 'yan takara.