Rikicin shugabanci ya barke a Zambiya
November 4, 2014Rikicin shugabanci ya barke a kasar Zambiya a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da zaman makokin tsohon shugaban kasa Michael Sata da ya rasu a makon da ya gabata a birnin London. Shugaban da ke rikon kwarya Guy Scott ya tsike babban abokin karawarsa Edgar Lungu daga mukaminsa a jam'iyyar Patriotic Front da ke mulki.
Sai dai kuma a lokacin da ya ke mayar da martani minista Lungu ya ce shugaba Scoot ya ci mutunci 'yan Zambiya da kuma al'adunsu, sakamakon haddasa rikicin siyasa da ya yi a daidai lokacin da ake tsaka da karramar gawar tsohon shugana kasa.
Matasa da dama ne suka fito kan tituna a birnin Lusaka, inda suka kona tayoyi domin nuna rashin amincewarsa da matakin tsige Lungu da aka yi.
Masu lura da abin da kan je ya zo a Zambiya sun nunar da cewar jam'iyyar PF da ke mulki za ta iya tsayar da Edgar Lungu a takarar shugabancin kasa, saboda shi ne dama shugaba Sata ya bar ma wuka da nama lokacin da ya ke jiyya. Yayin da shi kuwa Guy Scoot wanda bature ne kuma ke rikon kwarya ba zai iya tsayawa takara ba saboda iyayensa ba 'yan asalin Zambiya ba ne.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu